DA safiyar jiya Lahadi Allah ya ɗauki ran mahaifin tsohuwar jaruma a Kannywood, Hajiya Muhibbat Abdulsalam.
Malam Abdul’aziz Abdulsalam ya rasu da misalin ƙarfe 6:30 na safe a gidan sa da ke unguwar Ɗanladi Nasidi a Kano, bayan ya yi fama da jinya tsawon shekara biyu.
Marigayin, mai kimanin shekaru 92, ya rasu ya bar ‘ya’ya tara, maza shida, mata uku.
An yi jana’izar sa da misalin ƙarfe 10:00 na safe a unguwar Ɗanladi Nasidi, daga nan aka kai shi gidan sa na gaskiya a maƙabartar Tarauni.
Surukin marigayin, wato mijin Muhibbat, darakta Hassan Giggs, ya shaida wa mujallar Fim cewa Malam Abdulaziz Abdulsalam ya rasu ne a cikin gidan da ‘yar sa Muhibbat ta saya masa a kusa da gidan su a unguwar Ɗanladi Nasidi.
Haka kuma marigayin wanda shi ke riƙe da makullan Masallacin Madina da ke cikin unguwar, ya ba da wata wasiyya mai motsa zukata, wato da ya ce idan Allah ya ɗauki ran sa, a binne shi a maƙabartar Tarauni, inda a nan aka binne matar sa. Hakan kuwa aka yi. Allahu Akbar!

Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci jana’izar sun haɗa da Manajan Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), jarumi Ali Nuhu, da Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba Al-Mustapha, da furodusa Alhaji Sani Arrahus da darakta Malam Sadiq N. Mafia.
Allah ya rahamshe ahi, amin.