• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Takarar 2023: An maida Ali Nuhu gwamnan Kogi

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
September 19, 2021
in Labarai
2
Ali Nuhu ya hakimce a ofis a matsayin Gwamna Yahaya Bello

Ali Nuhu ya hakimce a ofis a matsayin Gwamna Yahaya Bello

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN tauraron Kannywood, Ali Nuhu, ya samu damar hawa matsayin gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a cikin wani fim ɗin Nollywood da ake ɗauka yanzu.

Shirin, mai suna ‘The White Lion’, ana shirya shi ne a garin Lokoja domin nuna irin gudunmawar da gwamnan ya bayar ga al’ummar jihar sa, musamman matasa da kuma ɓangaren harkokin siyasa.

Wasu ‘yan Nollywood ne ke shirya fim ɗin da harshen Turanci.

Gwamna Yahaya Bello (Ali Nuhu) ya na gabatar da jawabi a cikin ‘The White Lion’

Daraktan shirin shi ne Tunde Olaoye, wanda fitaccen mai bada umarni ne a Nijeriya. Ya yi daraktin finafinai da dama, kamar su ‘Bosun’s Empire’, ‘Lugard’, da kuma ‘Fools’ Day’, wanda zai fito a ranar 24 ga wannan watan na Satumba.

Ɗaya daga cikin manyan jaruman shirin na ‘The White Lion’ ita ce fitacciyar jarumar Nollywood ɗin nan, Roseanne Chikwendu, wadda ake ɗauka a matsayin matar gwamnan Kogi, wato Rashidat Yahaya Bello.

Hoton gwamna a cikin shirin

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Alhaji Yahaya Bello na daga cikin gwamnonin Arewa da ake raɗe-raɗin za su nemi takarar shugabancin ƙasar nan a shekarar 2023. 

Akwai hasashen cewa shirin ‘The White Lion’ wani ɓangare ne na tallafa wa burin gwamnan na zama shugaban ƙasa.

Roseanne Chikwendu a matsayin Rashidat Yahaya Bello a shirin ‘The White Lion’

Ali ya taɓa yin iƙirarin cewa wasu jaruman finafinan Hausa su ma su na da ƙudirin tsayawa takara a zaɓen ƙasar nan da ke tafe a cikin 2023.

Loading

Tags: 2023 electionsAli NuhuKannywoodnollywoodRashidat Yahaya BelloRoseanne ChikwenduThe White LionTunde OlaoyeYahaya Bello
Previous Post

Gyaran Dokar Zaɓe: Har yanzu Majalisar Tarayya ba ta amince da wasu manyan muradai ba – INEC, Yiaga Africa

Next Post

Akwai abu uku da ba zan manta ba game da mahaifiya ta, inji Fati S.U.

Related Posts

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza
Labarai

Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza

June 20, 2025
Next Post
Marigayiya Hajiya Hauwa (a hagu) da Fatima S.U. Garba

Akwai abu uku da ba zan manta ba game da mahaifiya ta, inji Fati S.U.

Comments 2

  1. Pingback: Jarumi Ali Nuhu ya Zama Gwamnan jihar Kogi a wani Shirin film Mai suna The White Lion – HausaLoaded.Com
  2. Shafiu Aliyu says:
    4 years ago

    Hum Allah yasa kwalliya tabiya kudin sabulu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!