• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 24, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2023: Abin da ya sa MOPPAN ta ke nema wa waɗanda aka ƙona wa kaya tallafi – Gidan Dabino

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
April 6, 2023
in Labarai
0
Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON

Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, ya bayyana cewa ƙungiyar ta kafa wani kwamiti da zai samar da gudunmawar kuɗi domin tallafa wa ‘yan fim waɗanda su ka yi asara a tarzomar bayan zaɓen gwamnan jihar domin rage masu raɗaɗin abin da ya same su. 

Ƙungiyar dai a karan kan ta ta bayar da gudunmawar N100,000, yayin da shugabannin ta kowanne ya bayar da N10,000, wanda a nan take su ka samar da jimillar kuɗi N220,000.

A lokacin da mujallar Fim ta nemi jin ta bakin sa, Gidan Dabino ya ce: “Su waɗannan ‘yan’uwan mu ne kuma abokan sana’ar mu ne, don haka duk wani abu da ya same su, to ya shafe mu. Don haka mu ka samar da wani kwamiti da zai haɗa ɗan abin da ya samu na tallafi domin a ba su don su ɗan samu sassaucin raɗaɗin abin da ya faru na mummunar asarar da su ka yi.

“Don haka kamar yadda wasu ƙungiyoyi na cikin Kannywood su ka yi, mu ma mun yi wannan yunƙurin, mu na sa ran a cikin wannan satin mu haɗa abin da mu ka samu mu gabatar masu da shi domin su ɗan samu abin da za su ɗan yi buƙatun azumi, wanda a yanzu kowa ya san halin da ake ciki, kuma sun samu kan su a yanayin ibtila’i, don ba ƙaramar asara aka yi ba wanda bayan an kwashe kayayyakin su wasu kuma an ƙone wajen nasu ne ƙurmus, don haka mu ka ƙudiri aniyar tallafa masu, wanda har yanzu ƙofa a buɗe ta ke, mu na neman gudunmawar kowa da kowa.”

Ƙone kayan dai da fashe-fashe ya shafi ofisoshi huɗu ne – na Dauda Rarara, Baban Chinedu, Ahmad M. Sadiq, da Rabi’u The King wanda shi ne aka ƙone shi ƙurmus bayan an kwashe kayayyakin da ke ciki.

Irin wannan abu da ke biyo bayan fitar da sakamakon zaɓe ga ‘yan fim a Kano ba sabon abu ba ne. A cikin 2011 da aka bayyana Shugaban Ƙasa Jonathan a matsayin wanda ya ci zaɓe, an farfasa wajen Nura Hussaini da Baba Ƙarami, sannan aka yi ta farautar Sani Danja za a kashe shi saboda ɗan PDP ne a lokacin, wanda har sai da ta kai shi ga barin Kano ya tare a Abuja.

Loading

Tags: Ado Ahmad Gidan Dabinogwamnan KanoMOPPANtallafitarzomaZaɓen 2023
Previous Post

Ƙungiyar Mawaƙa Mata na Kannywood taron macuta ne, ba inda za ta je – Fa’iza Badawa

Next Post

Yadda rikicin kuɗi ya farraƙa sabuwar ƙungiyar mawaƙa mata – Fati Kawo

Related Posts

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
Next Post

Yadda rikicin kuɗi ya farraƙa sabuwar ƙungiyar mawaƙa mata - Fati Kawo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!