ƊIMBIN masu harkar finafinan Hausa sun shiga sahun sauran al’ummar Musulmi a faɗin Nijeriya wajen yin tofin Allah-tsine da jaridar nan ta intanet mai suna ‘Sahara Reporters’.
Jaridar, wadda mallakin wani ɗan Nijeriya mai gwagwarmayar ‘yancin ɗan’adam mai suna Sowore ce, ta wallafa wani labari ne a kan ɗan gwagwarmayar tabbatar da samuwar ƙasar Yarabawa mai cin gashin kan ta ɗin nan mai suna Sunday Igboho, inda ta ruwaito ƙungiyar Afenifere ta na kwatanta shi da fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW).
Jaruman Kannywood da dama sun yi Allah-wadai da jaridar da mawallafan ta.
Mujallar Fim ta tattaro wasu daga cikin kalaman ɓacin rai da ‘yan fim su ka wallafa a soshiyal midiya.
A yayin da wasu sun yi rubutu kai tsaye, wasu kuma sun tura ‘hashtag’ ɗin ‘No to Sahara Reporters’ ne don bayyana rashin jin daɗin su. Wasu kuma sun daina bin shafukan jaridar a soshiyal midiya.
Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Isma’il Na’abba (Afakallah), ya rubuta amshin waƙar Shata mai cewa, “Na tsaya ga Annabi Muhammadu (S.A.W.)”.
Shi kuma jarumi Abba El-Mustapha sai ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’una! Wannan ɓatanci da aka yi wa Shugaba Annabi Muhammadu S.A.W. ya yi yawa. Allah ya tsine wa kamfanin Sahara Reporters da duk maƙiyin addinin Musulunci.
“Bayan mun la’ance su tare da yanke duk wata mu’amala, sai mu miƙa koken mu ga manhajar da ta ba su damar yaɗawa.
“Mu na kira ga gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta ɗaukar dukkan matakan hukunta kamfanin Sahara Reporters.
“Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga Annabi Muhammad S.A.W. da alayen sa da sahabban sa baki ɗaya.”
Shi kuwa marubuci Ibrahim Birniwa cewa ya yi, “A dinga yin ‘hashtag’ yayin da mu ke Allah-wadai da Sahara Reporters. Shi ne zai jawo hankalin Instagaram su ɗauki mataki.”
Mawaƙi Ali Jita kuma ya ce, “Tir da Sahara Reporters! Ina yi musu fatan haɗuwa da fushin Ubangiji a nan duniya da kuma ƙiyama.”
Ita kuwa Fati Abubakar (Shu’uma) cewa ta yi, “Allah ya tsine wa duk wani wanda ya ke taimaka wa Sahara Reporters ta fili ko ta ɓoye.”

A nasa martanin, Baballe Hayatu ya ce: “Allah ya tarwatsa ku da duk mai hannu a abin da ku ke yi, Sahara Reporters. Ya Allah ya kwashe duk wata ni’ima a cikin Sahara ya halicce ta a buhel. Kuma Allah ya yi muku. Ya sa suna da lamuran ku ya zama kamar yadda Allah ya halicci Sahara Desert. Allah ya kwashe duk wata albarka a lamuran ku da abin da ya kusance ku.
“Don Allah kowanne Musulmi in ya na bin su to ya yi ‘unfollowing’ ɗin su tsinannu.”
Ali Nuhu kuma ya ɗauko abin da Abdul Amart Mai Kwashewa ya yi ne ya sake wallafawa, wato da ya ce: “Tir da Sahara Reporters! Ina yi musu fatan haɗuwa da fushin Ubangiji a nan duniya da kuma ƙiyama.”
Misbahu AkA Anfara kuma ya ce: “Kai duniya kenan! Dole ne Igboho ya yi mutuwar wulaƙaci… Allah ya nutsar da ku kamar yadda ya yi wa mutanen Annabi Lut! Annabi ya fi ƙarfin a kwatanta shi da duk wani halittar Allah a ban ƙasa! In Allah ya yarda wannan abin da aka yi wa shugaban duniya Annabi Muhammad S.A.W. sai fushin Allah ya sauka…”
Shi ma darakta Sheik Isa Alolo cewa ya yi, “Tir da Sahara Reporters! Ina yi musu fatan haɗuwa da fushin Ubangiji a nan duniya da kuma ƙiyama.”
Furodusa Alhaji Sheshe tare da Daddy Hikima kuma su ka ce, “Mu na Allah-wadai da wannan gidan jaridar na Sahara Reporters bisa rubutun ɓatancin da su ka yi a kan Annabin mu abin koyin mu abin alfaharin mu kuma abin koyin mu.
“Ya Rabbi, mu na roƙon ka da kyawawan sunayen ka mafiya kamala, ya Allah ka tarwatsa wannan gidan jaridar, ka hana su jin daɗin rayuwar su duniya da lahira su da magoya bayan su da duk wanda ya ji daɗi bisa rubutun da su ka yi. Ya Allah ka tsine musu albarka.
“Ana uhibbuka ya Rasulullah bi da ka abi wa ummi ya Rasulullah. Rai na fansa gare ka ni da iyaye na Ma’aikin Allah.”
Adam A. Zango kuma ya ce, “Mu yi amfani da yawan mu wajen kare martaban Manzon Allah S.A.W. (Say No To Sahara Reporters).”
Sai dai a lokacin da ake haɗa wannan rahoton tuni jaridar ta Sahara Reporters, wadda ake bugawa daga birnin New York na ƙasar Amurka, ta cire labarin daga gidan yanar ta sannan kuma ta bada haƙuri ga ɗaukacin Musulmi.
A cewar jaridar, ba ita ce ta ƙirƙiri maganar da ta ɓata wa Musulmi rai ba, ƙungiyar Afenifere ce; ita kawai ta ruwaito maganar ƙungiyar ne.
Ta ce ita jarida ce mai girmama kowane addini ba tare da nuna bambanci ba.
![]()







