• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

An yi dakan ɗaka shiƙar ɗaka a auren ɗan shugaban MOPPAN, Najib Habibu Barde, da amaryar sa A’isha

by ABBA MUHAMMAD
February 26, 2024
in Ranar Murna
0
An yi dakan ɗaka shiƙar ɗaka a auren ɗan shugaban MOPPAN, Najib Habibu Barde, da amaryar sa A’isha

Najib Habibu Barde a kan doki lokacin kilisa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN riƙo na Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Habibu Barde Mohammed, ya bayyana cewa auren zumunci ne aka ƙulla tsakanin ɗan sa Najib da sahibar sa A’isha a ranar Asabar.

Ya bayyana haka ne a hirar sa da mujallar Fim kan auren Najib Habibu Barde da abar ƙaunar sa A’isha Aminu Saley da aka ɗaura a safiyar shekaranjiya Asabar a gidan marigayi Malam Suley Ɗan Gogel da ke Layin Faruk Mustapha, daura da Layin Alhaji Sarauta, a Azare, Jihar Bauchi.

An yi walimar cin abinci a gidan mahaifin angon da ke GRA, Azare, bayan ɗaurin auren.

Ana ɗaura auren Najib da A’isha
Najib (na 2 daga hagu, sanye da gilashi) da mahaifin sa (na 3 daga dama) da iyaye

Haka kuma a ɓangaren gidan amarya, an yi walima ta mata a gidan mahaifin amarya, Alhaji Aminu Suley, wanda tsohon Mataimakin Shugaba (DCG) ne na Hukumar Kurkuku ta Nijeriya.

An kai amarya gidan ta bayan ango da abokan sa sun yi kilisa kan dawakai a yammacin ranar, wanda ya ƙayatar sosai.

Alhaji Habibu Barde Mohammed ya shaida wa mujallar Fim cewa auren haɗin gida aka yi, wato auren zumunci, domin kuwa mahaifin amaryar kawun shi mahaifin angon ne.

Wato dai an yi abin da Hausawa ke ce wa “dakan ɗaka shiƙar ɗaka”.

Daga hagu: Hamisu Iyan-Tama, Ahmad Sarari, Habibu Barde, da Nasiru Gwangwazo

Haka kuma ya ce, “Mu na godiya ga dukkan waɗanda su ka halarci bikin tare da ɗaurin auren.

“Allah ya saka da alheri, ya bar zumunci, amin summa amin.

“Jiya Lahadi dukkan baƙi kowa ya koma gida lafiya lau. Mun gode wa Allah (s.w.t).”

Waɗanda su ka wakilci ‘yan Kannywood sun haɗa Alhaji Hamisu Iyan-Tama, Dakta Ahmed Sarari da Malam Nasiru Gwangwazo.

To, Allah ya ba Najib da A’isha zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

‘Yan’uwa da abokan arziki su na gaisawa da baban ango
Najib Habibu Barde a tsakiyar abokan sa

Loading

Tags: A'isha Aminu SuleyAzareɗaurin aureHabibu Barde MuhammadNajib Habibu Barde
Previous Post

Kotun Kano ta ba da umarnin a kamo mata Ado Gwanja

Next Post

Hajiya Hannatu, uwa ga tsohuwar jarumar Kannywood Halima Adamu Yahaya, ta rasu

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post

Hajiya Hannatu, uwa ga tsohuwar jarumar Kannywood Halima Adamu Yahaya, ta rasu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!