• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

‘Yan Kannywood sun taya jaruma Radeeya Jibrin murna kan auren bazata

by MUKHTAR YAKUBU
May 31, 2026
in Ranar Murna
0
‘Yan Kannywood sun taya jaruma Radeeya Jibrin murna kan auren bazata

Radeeya Jibril

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

‘Yan Kannywood da dama sun taya jaruma Radeeya Jibrin murna bayan ta ba da sanarwar bazata cewa ta yi aure.

Da alama, ta yi auren ne cikin sirri ba tare da sanar da kowa ba.

A yau Lahadi ne ta ba da sanarwar a shafin ta na Facebook.

A saƙon nata, ta bayyana tsananin yadda take son zaman aure a wannan lokacin ko don ‘ya’yan ta. Ta bayyana hakan ne bayan an sake ɗaura mata aure yau.

A cikin wani saƙon, jarumar ta ce: “Alhamdu lillah. Alhamdu lillah. Alhamdu lillah. Allah ka fi kowa sanin dalili na na son aure kuma na san duk wata jarabawa ta a kan aure kaine kake ɗora mini. Sannan kuma kai ne kake ƙara ƙaddara mini yin aure a lokacin da ka so. Allah na gode maka da wannan jarabawar taka a gare ni.

“Allah yadda na yi tawassali da kai, na yi imani da kai, na yarda da wannan auren domin ka domin gobe na domin yara na domin ‘yan’uwa na domin mahaifi na domin lahira ta.

“Allah ubangiji ka ba ni ikon ƙare rayuwa ta a ɗakin miji na. Allah Ubangiji ina roƙon ka don girman ka, don tsarkin ka don rahamar ka don darajar fiyayyen halitta Manzo sallallahu alaihi wasallam, Allah ubangiji ba don hali na ba, Allah yadda aka ɗaura mini aure yau, Allah Ubangiji ka sa sai dai a fitar da gawa ta a ɗakin miji na. Bissalam.”

Bayan ta wallafa sakon nata, ‘yan fim da ɗimbin masoyan ta sun taya ta murna da yi mata, tare da fatan Allah ya karɓi addu’ar ta kamar yadda ta rubuta cikin nuna neman yardar ta ga Ubangiji.

Jarumi Ali Nuhu ya taya ta murna tare da yi mata addu’ar Allah ya cika mata burin ta na zama a ɗakin mijin ta har ƙarshen rayuwar ta.

Shi ma Baballe Hayatu ya taya ta murna tare da yi mata fatan alheri.

Jaruma Saratu Abubakar kuma cewa ta yi: “Ba mu da abin da za mu ce sai Alhamdu lillah! In-sha Allah daga nan duniya till Janna, Radeeya Jibril. Congratulations once again.”

Shi ma jarumi Umar Gombe cewa ya yi: “Radeeya Jibril – Allah Ya ba ki zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba. Amin.”

Radeeya Jibril

Furodusa Sani Arrahus shi ma ya bayyana a shafin kamfanin sa kamar haka: “Muna farin cikin sanar da auren Radeeya Jibril wadda aka ɗaura a yau Lahadi.

“Muna mata fatan alkhairi. Ubangiji Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba albarkacin Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam. Ubangiji Allah ka kau da dukkan sharri.”

Loading

Tags: auremurnaRadeeya Jibril
Previous Post

MOPPAN ta yi alhinin rasuwar tsohuwar jarumar Kannywood Wasila Isma’il

Next Post

Masu aibanta ni kan Wasila ku tuba ku daina – Ciroma

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post
Masu aibanta ni kan Wasila ku tuba ku daina – Ciroma

Masu aibanta ni kan Wasila ku tuba ku daina - Ciroma

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!