• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, October 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tallar Tinubu: Mansurah Isah ta dawo daga rakiyar Rarara

by MUKHTAR YAKUBU
June 28, 2026
in Labarai
0
Tallar Tinubu: Mansurah Isah ta dawo daga rakiyar Rarara

Mansurah Isah da Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jaruma kuma furodusa a Kannywood, Hajiya Mansurah Isah ta fice daga ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope, wadda ke goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bayan wani saɓani da ya ɓarke tsakanin ta da shugabannin ƙungiyar.

Rahotannin da mujallar Fim ta samu sun nuna cewa saɓanin ya samo asali ne bayan wata tafiya da membobin ƙungiyar suka yi zuwa Abuja a kwanakin baya.

Majiyoyi sun bayyana cewa bayan kammala taron da suka halarta, Mansurah ta samu wata gayyata ta daban, inda aka buƙaci ta halarta tare da wasu daga cikin mutanen da ke tare da ita.

A cewar majiyoyin, jarumar ta nemi ta tafi da wasu daga cikin membobin da suka yi tafiyar Abuja tare da ita. Sai dai shugabannin ƙungiyar sun nuna rashin amincewa da hakan, suna mai cewa duk wata halarta ta irin wannan ya kamata ta kasance da sunan ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope, ba da sunan mutum ɗaya ba.

Rahoton ya ce Mansurah ta nuna rashin gamsuwa da wannan matsaya, tana mai cewa ita ce aka gayyata kai-tsaye, don haka tana da damar zaɓar waɗanda za su raka ta.

Majiyoyin sun ce rashin daidaituwar fahimta kan wannan batu ne ya haifar da saɓanin da ya kai ga ficewar jarumar daga ƙungiyar.

Ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope ta haɗa jaruman finafinai, mawaƙa, furodusoshi, daraktoci da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood domin tallafa wa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Alhaji Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) shi ne mai jagorantar ƙungiyar a matakin ƙasa, yayin da jarumi Lawan Ahmad yake riƙe da shugabancin reshen Kannywood.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a rubuce daga Mansurah ko shugabannin ƙungiyar da ke tabbatar da ko musanta faruwar lamarin.

Loading

Tags: Dauda Abdullahi Kahutu RararaƙungiyaMansurah Isahsiyasa
Previous Post

Jaruman Kannywood sun cika Rimin Gado a bikin auren ‘yar Halima Adam Yahaya

Next Post

Furodusan Kannywood Alhaji Sheshe zai angwance ranar Asabar

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Furodusan Kannywood Alhaji Sheshe zai angwance ranar Asabar

Furodusan Kannywood Alhaji Sheshe zai angwance ranar Asabar

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!