• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2027: Ƙungiyar siyasar ‘yan Kannywood za ta yi taron nuna goyon baya ga Gwamnan Kano

by MUKHTAR YAKUBU
July 4, 2026
in Labarai
0
Zaɓen 2027: Ƙungiyar siyasar ‘yan Kannywood za ta yi taron nuna goyon baya ga Gwamnan Kano

Alhaji Isma'il Khalil Ja'en Mahy

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WATA ƙungiyar siyasa ta ‘yan fim a Kano mai suna Kannywood Awareness Network for Abba Gida Gida, ta bayyana shirin ta na gudanar da babban taron nuna goyon baya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a watan gobe.

Shugaban ƙungiyar, fitaccen darakta Isma’il Khalil Ja’en Mahy, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai kan manufofi da ayyukan ƙungiyar.

A cewar sa, an kafa ƙungiyar ne domin samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnatin jihar da Kannywood, tare da tabbatar da cewa masu harkar finafinan Hausa suna cikin waɗanda ke amfana da duk wani shiri na bunƙasa harkokin al’adu da masana’antu.

Ya ce: “Ƙungiyar tana da manufofi da tsare-tsare masu yawa da za su taimaka wajen cigaban masana’antar Kannywood. Mun kafa ta ne domin mu haɗa kai da gwamnati, ta yadda idan aka tsara shirye-shiryen cigaban masana’antu, Kannywood ma za ta kasance cikin masu cin gajiyar waɗannan tsare-tsare.”

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taron ƙungiyar a watan Agusta, inda za a bayyana manufofin ta da irin alaƙar da take da Gwamnatin Jihar Kano.

Isma’il ya ce taron zai kuma zama wata dama ta nuna goyon bayan ƙungiyar ga gwamnan, bisa abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin gwamnatin sa wajen bunƙasa masana’antar Kannywood.

Ya ce: “Za mu bayyana irin cigaban da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kawo wa masana’antar Kannywood. Wannan ne ya sa muke ci gaba da mara masa baya, tare da fatan zai ci gaba da samar da manufofin da za su ƙara bunƙasa masana’antar domin amfanin masu sana’ar yanzu da kuma waɗanda za su zo nan gaba.”

Daraktan ya jaddada cewa ‘yan Kannywood a ƙarƙashin ƙungiyar sun himmatu wajen haɗa kai domin samar da duk wani tsari da zai inganta masana’antar finafinan Hausa.

A cewar sa, babban manufar taron ita ce sake tabbatar da cikakken goyon bayan ƙungiyar ga gwamnan, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da industiri.

Loading

Tags: Gwamna Abba Kabir YusufIsma'il Khalil Ja'en MahyKannywoodƙungiyasiyasazaɓen2027
Previous Post

Zaɓen 2027: Jarumi Rabi’u Rikadawa ya bi sahun masu daina bin Rarara, ya fice daga ƙungiyar Triple R

Next Post

Amal Umar za ta fara aikin sabon fim da jarumin Nollywood

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Amal Umar za ta fara aikin sabon fim da jarumin Nollywood

Amal Umar za ta fara aikin sabon fim da jarumin Nollywood

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!