• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zaɓen 2027: Jarumi Rabi’u Rikadawa ya bi sahun masu daina bin Rarara, ya fice daga ƙungiyar Triple R

by MUKHTAR YAKUBU
July 3, 2026
in Labarai
0
Zaɓen 2027: Jarumi Rabi’u Rikadawa ya bi sahun masu daina bin Rarara, ya fice daga ƙungiyar Triple R

Alhaji Rabi'u Rikadawa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMIN masana’antar Kannywood, Alhaji Rabi’u Rikadawa, ya ba da sanarwar ficewar sa daga ƙungiyar siyasa ta Triple R Kannywood for Renewed Hope, inda ya zama sabon memba da ya bar ƙungiyar cikin ‘yan kwanakin nan.

Rikadawa ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a yau Juma’a, inda ya ce ya fice daga ƙungiyar ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe.

Sai dai jarumin bai bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar barin ƙungiyar ba.

Kafin ficewar tasa, wasu fitattun jaruman da suka haɗa da Mansurah Isah, Ibrahim Birniwa, Abdulkareem Papalaje da Fati K.K. sun riga sun ba da sanarwar ficewar su daga ƙungiyar.

An kafa Triple R Kannywood for Renewed Hope ne domin haɗa jaruman Kannywood da sauran masu nishaɗi masu goyon bayan jam’iyyar APC da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.

Fitaccen mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) shi ne jagoran ƙungiyar. Da yawa sun ce ƙarfin ikon da yake da shi a ƙungiyar ta sa sauran membobin ta sun zama hoto kawai, sai abin da ya ga dama ake ƙullawa.

To amma duk da ficewar tasu daga ƙungiyar, da dama daga cikin waɗanda suka bayyana barin Triple R sun jaddada cewa ba su fice daga APC ba. Sun ce za su ci gaba da mara wa jam’iyyar baya, sai dai ba a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar ba.

Loading

Tags: Dauda Abdullahi Kahutu RararaKannywoodRabi'u RikadawasiyasaTriple Rzaɓen 2027
Previous Post

Ƙungiyar Rarara ta ɗauki nauyin aikin ƙanwar jaruma Fati Al-Amin a asibiti

Next Post

Zaɓen 2027: Ƙungiyar siyasar ‘yan Kannywood za ta yi taron nuna goyon baya ga Gwamnan Kano

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Zaɓen 2027: Ƙungiyar siyasar ‘yan Kannywood za ta yi taron nuna goyon baya ga Gwamnan Kano

Zaɓen 2027: Ƙungiyar siyasar 'yan Kannywood za ta yi taron nuna goyon baya ga Gwamnan Kano

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!