SAUKAR karatun Alƙur’ani wani abu ne da yake da falala da tarin daraja da girma, kuma ya na ɗaya daga cikin abubuwa guda uku da Manzon Allah (s a w.) ya ce mu ladaftar da ‘ya’yan mu – wato son Manzon Allah da son iyalan gidan sa da kuma karatun Alƙur’ani.
Jarumi a Kannywood, Umar Sani Jigirya, wato Sallau a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’, ya cika da farin ciki a lokacin bikin saukar karatun Alƙur’ani da ‘ya’yan sa Mu’azzam da Aliyya su ka yi.
A ranar Lahadi, 1 ga Janairu, 2023 aka yi taron bikin saukar karatun wanda jama’a da dama su ka halarta domin taya shi murna.
Da yake bayyana farin cikin sa ga mujallar Fim, Malam Umar ya ce:

“Alhamdu lillah, ina godiya ga Allah da ya kawo mu ga wannan rana da aka yi taron bikin saukar karatun Alƙur’ani da ‘ya’ya na su ka yi.
Wannan abin farin ciki ne a gare ni da dukkan Musulmi. Don haka ina godiya ga dukkan jama’ar da su ka taru a wannan wajen taron, Allah ya ba mu damar sauke nauyin da ya ke kan mu na tarbiyyar ‘ya’yan mu albarkacin Annabi da Alƙur’ani.”
![]()








Comments 1