BAYAN fita daga jam’iyyar ADP da ajiye takarar Majalisar Wakilai a Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano da ya yi a farkon wannan makon, a yanzu dai mawaƙi Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Mawaƙin kuma ɗan siyasar ya samu damar ganawa da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, a daren jiya Juma’a.
A wani faifan bidiyo da ya saki a yau, wanda wakilin mujallar Fim ya kalla, Ala ya bayyana tattaunawar da su ka yi da Gawuna a matsayin wata alaƙa ta tafiya tare don ganin ya samu nasarar zama gwamna a zaɓe mai zuwa.

Haka kuma ya bayyana cewa tuni aka saka shi a cikin ‘yan yaɗa manufa tare da tallar tafiyar Gawuna ɗin.
Ala ya yi kira ga masoya da kuma magoya bayan sa, musamman na mazaɓar sa, da su goya masa baya.
Shigar Ala APC ta zo da bazata, musamman idan aka dubi tsamin dangantakar da ke tsakanin sa da gwamnatin Jihar Kano tun daga bayan zaɓen 2019 inda ya yi tafiyar Kwankwasiyya, wanda ake ganin shi ya jawo har gwamnatin jihar ta so ta tura shi gidan yari bisa zargin ya fitar da waƙa ba tare da an tace ta ba.