• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, November 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

* Tare da shi muka kafa masana'antar tun kafin a raɗa mata sunan Kannywood, inji Iyan-Tama

by ALI KANO
February 22, 2026
in Labarai
0
Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

Marigayi Alhaji Nura Shareef

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ALLAHU Akbar! Allah ya yi wa ɗaya daga cikin dattawan Kannywood, Alhaji Nura Shareef Ibrahim, rasuwa a daren yau.

Nura dai furodusa ne, edita, jarumi kuma darakta a masana’antar, kuma da shi aka kafa ta tun farkon ta.

‘Yan fim da dama sun kaɗu da jin labarin rasuwar tasa, kuma sun yi masa addu’a.

Sakataren ƙungiyar masu shirya finafinai ta KAFIGAN reshen Jihar Kano, Malam Sani Ahmed Kankarofi, ya ba da sanarwa a madadin shugaban ƙungiyar reshen jihar, Alhaji Isah A. Isah, cewa za a yi masa jana’iza gobe da safe da ƙarfe 10 a gidan su, wato gidan Sharif Hamidan, da ke unguwar Ɗandago Sabon Titi, layin da ke kallon Islamiyyar Abu Hanifa.

Ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya sa Aljanna ce makomar sa.

Da yake bayyana rasuwar, babban furodusa Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, ya ba da labarin yadda aka kafa masana’antar Kannywood tare da marigayin, da irin rawar da yake takawa a cikin ta tun daga farkon ta har zuwa ƙarshen rayuwar sa.

A rubutun ta’aziyyar da ya yi a Facebook, Iyan-Tama ya bayyana cewa: “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un. Ku saka shi cikin addu’o’in ku.

“Nura Shareef. Sharifi ne. Film editor ne tun lokacin linear, wato babu komfuta, kuma camera man ne, daga baya ya zama furodusa/darakta.

“Ya yi editin/furodusin da daraktin na finafinan Hausa da dama.

“Na yi aiki da shi kusan shekaru masu yawa. Lokacin da zan buɗe kamfanin Iyan-Tama Multimedia da shi muka assasa kamfanin.

“Abokin ƙani na ne Auwalu Iyan-Tama, sun yi Sharaɗa Secondary School tare.

“Auwalu ne ya gabatar mun da shi cewa ya ji an ce zan buɗe kamfanin multimedia na audio/visual production don in ba shi aiki, kuma na ɗauke shi.

“Nura Sharif ya yi aiki da Garun Malam Video Club da ke Sabon Titin Mandawari na Alhaji Garba kafin zuwan sa Iyan-Tama Multimedia. Garun Malam Video Club na bayar da hayar finafinai na Indiya da sauran su, da dubbing na video cassette, rentals da video coverage na ɗaurin aure ko biki ko ɗaukar karatun Alƙur’ani a wancan lokaci. Suna da video cameras domin ba da haya.

“Raina Kama na Ɗan’azumi Baba Ceɗiyar ‘Yangurasa, wato Kamaye, da Garun Malam Video Club tare suka shirya fim ɗin da na fara fitowa na yi aktin a commercial film kusan a shekarar 1993/94/95, wato fim ɗin ‘Bakandamiyar Rikicin Duniya’. A nan na fara sanin Nura Shareef.

“Da shi aka kafa masana’antar shirya finafinai ta Hausa – Kannywood. Kusan kowa a gaban sa ya zo illa nadiran.

“Muna tare tun babu sunan ‘Kannywood’.

“Shi ne mutum na farko da ni da Ɗan’azumi Baba muka miƙa wa mukullan Iyan-Tama Multimedia a 1996. Shi yake buɗewa kuma shi yake rufewa, kuma a wajen sa ake yin booking ɗin duk wani abu da za a gabatar a Iyan-Tama Multimedia, wato shi ne manaja.

“Saboda natsuwar sa da hankalin sa na shirya masa fim ɗin ‘Fallasa’ shi da Wasila Isma’il da Ɗan Ibro da Bankaura da Ishaq Sidi Ishaq, wanda marigayi Tijjani Ibrahim ya ba da umarni.

“Nura Shareef kullum cikin fara’a. Da wuya ka ga fushin sa.

“Kafin rasuwar sa ya yi ayyuka da kamfanonin fim da dama, ciki har da babban kamfanin shirya finafinai na Sarari Classic na Dakta Sarari, sannan kuma a wannan shekarar da ta gabata, 2025, ya yi ayyuka da babban kamfanin shirya finafinai na Abnur Entertainment, kamfanin Abdul Amart Maikwashewa. Har rasuwar sa suna tare da Abdul Amart.

“Nura Shareef mutum ne mai juriya da haƙuri da sanin mutuncin mutane.

“Yanzun nan na buɗe waya ta na ga saƙo daga Auwalu Indabawa, ya sanar da ni rasuwar sa.

“Allah ya jiƙan jikan sa, ya yi masa rahama.”

Shi kuwa tsohon Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Dakta Ahmad Sarari, ya ce sun shafe tsawon shekaru 23 tare da marigayin.

A ta’aziyyar da ya yi da Turanci a Facebook, wadda mujallar Fim ta fassara, cewa ya yi: “A yau ina jimamin rasuwar wani ɗan’uwa, aboki kuma abokin aiki na, Nura Sharif Ibrahim. Mun yi tafiya mai ma’ana tare, muna aiki kafaɗa da kafaɗa a wannan ƙungiya guda har tsawon shekaru 23.

“Allah Ya jiƙan sa da rahama, Ya sa ya huta a Aljannatul Firdausi.

“Ina roƙon Allah Ya albarkaci iyalan sa, Ya tsare su, Ya kuma kula da su a wannan lokaci mai wuya da ma bayan haka. Ameen, Ya Rabbi.”

Loading

Tags: HamisuIyantamaKAFIGANKannywoodNuraShareefrasuwa
Previous Post

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

Next Post

Rasuwar jarumar Kannywood Wasila Isma’il ta girgiza jama’a

Related Posts

Fitacciyar marubuciya Jamila Umar Tanko ta rasu a Masar
Labarai

Fitacciyar marubuciya Jamila Umar Tanko ta rasu a Masar

November 20, 2026
KILAF 2026: Za a fara taron finafinan harsunan Afrika jibi Talata
Labarai

KILAF 2026: Za a fara taron finafinan harsunan Afrika jibi Talata

November 8, 2026
Zuwairiyyah Girei ta zama Manajar Darakta ta gidan talbijin na Mahanga mallakin jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi
Labarai

Zuwairiyyah Girei ta zama Manajar Darakta ta gidan talbijin na Mahanga mallakin jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi

November 2, 2026
Hotunan taron Tozali Henna Ball da karramawa
Labarai

Hotunan taron Tozali Henna Ball da karramawa

November 1, 2026
Isa Ja ya karɓi kyautar Tozali, yayin da Naziru da Amal suka ƙaurace
Labarai

Isa Ja ya karɓi kyautar Tozali, yayin da Naziru da Amal suka ƙaurace

October 31, 2026
Sauran kwana 7 a karrama Isa Ja, Naziru Sarkin Waƙa, Hausa Guy, da Amal Umar a bikin Henna Ball da Kyaututtukan Tozali a Abuja
Labarai

Sauran kwana 7 a karrama Isa Ja, Naziru Sarkin Waƙa, Hausa Guy, da Amal Umar a bikin Henna Ball da Kyaututtukan Tozali a Abuja

October 24, 2026
Next Post
Rasuwar jarumar Kannywood Wasila Isma’il ta girgiza jama’a

Rasuwar jarumar Kannywood Wasila Isma’il ta girgiza jama'a

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!