• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kannywood ta samu tallafin inshorar lafiya, marasa lafiya shida za su ci gajiya kai-tsaye

* Mu tattaru mu gode wa Abba El-Mustapha, cewar Salisu Officer

by MUKHTAR YAKUBU
June 6, 2026
in Labarai
0
Kannywood ta samu tallafin inshorar lafiya, marasa lafiya shida za su ci gajiya kai-tsaye

Alhaji Abba El-Mustapha tare da wasu daga cikin 'yan fim bayan an gama taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon shiri na inshorar lafiya ga masu harkar finafinai ta hanyar haɗin gwiwar Hukumar Tace Finafinai da Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kano (KCHMA), inda aka fara da ɗaukar nauyin kula da lafiyar wasu marasa lafiya shida daga cikin ’yan masana’antar.

An cimma wannan matsaya ne a wani taron haɗin gwiwa da aka gudanar tsakanin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kano (KCHMA) tare da shugabannin ƙungiyoyin masu harkar finafinai a ofishin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano a jiya Juma’a, 5 ga Yuni, 2026.

Da take jawabi a taron, Shugabar KCHMA, Dakta Rahila Aliyu Mukhtar, ta tabbatar da aniyar hukumar ta na yin aiki tare da Hukumar Tace Finafinai domin samar da tsarin da zai kula da lafiyar jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar finafinai ta jihar.

Ta bayyana cewa shirin zai taimaka wajen rage nauyin kuɗaɗen jinya da masu harkar finafinai suke kashewa, musamman waɗanda ke fama da cututtuka masu tsanani da ke buƙatar kulawa ta musamman.

Dakta Rahila Aliyu Mukhtar tana jawabi a taron. A gefen ta, Alhaji Abba El-Mustapha ne.

Shi ma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya ce wannan haɗin gwiwa yana daga cikin matakan da hukumar take ɗauka domin inganta walwala da cigaban masu harkar finafinai a jihar.

A nasu ɓangaren, shugabannin ƙungiyoyin Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) da Arewa Films Makers Association of Nigeria (AFMAN), Shehu Hassan Kano da Salisu Muhammad Officer, sun bayyana jindaɗin su tare da nuna cikakken goyon bayan su ga wannan shiri.

Sun yaba wa El-Mustapha bisa ƙoƙarin da ya yi na samar da wannan dama, musamman a lokacin da wasu daga cikin ’yan fim suke fama da matsalolin lafiya.

Ɗaya daga cikin ‘yan fim masu fama da rashin lafiya, Malam Aminu Awaisu Gaya (Mahiru), a wajen taron

A wani ƙarin bayani da ya yi a safiyar yau Asabar, Salisu Officer, ya bayyana cewa: “Bisa ƙoƙari da jajircewar ɗan’uwan mu, Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, tare da Shugabar KCHMA, Hajiya Rahila Aliyu Mukhtar, an samar wa masana’antar Kannywood wata gidauniyar jinƙai a fannin lafiya mai suna Kannywood Abba Care.

“Bayan zaman da aka yi tsakanin Hukumar Tace Finafinai, masu ruwa da tsaki na Kannywood, hukumomin biyu da kuma wasu masu fama da rashin lafiya guda shida a cikin masana’antar, an amince da ɗaukar nauyin kula da lafiyar su gaba ɗaya ba tare da sun biya ko kwabo ba.

“Haka kuma, an kafa wani kwamiti da zai tsara hanyoyin da duk ’ya’yan masana’antar Kannywood za su ci gajiyar wannan tsari cikin sauƙi, gaskiya da aminci.”

Daga dama: Zakiyya Ibrahim, Ladidi Fagge, da Hajiya Zahra’u (Adamar Kamaye) a taron

Officer ya yi kira ga dukkan ’yan Kannywood da su haɗa kai wajen yaba wa El-Mustapha bisa wannan gagarumar gudunmawa.

Ya ce: “Mu tattaru mu yaba wa Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano bisa samar da wannan gagarumar gudunmawa wadda tarihi ba zai taɓa mantawa da ita ba.”

Jagororin taron, Alhaji Abba El-Mustapha da Dakta Rahila Aliyu Mukhtar, bayan kammala taron

Loading

Tags: Abba El-MustaphaDakta Rahila Aliyu MukhtarHukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kano (KCHMA)Hukumar Tace Finafinaikiwon lafiyaSalisu Mohammed Officer
Previous Post

Yadda mutane suke kallon harkar fim daga waje ba haka take ba – Hafsat Ja’afar

Next Post

Ƙungiyar Matasa ta Ahmadu Bello ta karrama jarumar Kannywood Amal Umar da lambar yabo

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Ƙungiyar Matasa ta Ahmadu Bello ta karrama jarumar Kannywood Amal Umar da lambar yabo

Ƙungiyar Matasa ta Ahmadu Bello ta karrama jarumar Kannywood Amal Umar da lambar yabo

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!