A YAU Talata ne Allah ya yi wa babbar ‘ya ga darakta a Kannywood, Ismael Khalil Ja’en, Sa’adatu, rasu.
Ta rasu a Kano bayan ta sha fama da rashin lafiya, tana da shekaru 13 a duniya.
An ji jana’izar ta da yamma a gidan su da ke unguwar Ja’en a cikin garin Kano.
Jama’a da dama sun halarci jana’izar tare da yi wa Ismael Khalil Ja’en ta’aziyya.
Allah ya jikan ta, ya bai wa iyaye da ‘yan’uwa haƙurin juriyar rashin da aka yi.
![]()







