FURODUSA a Kannywood, Sultan Abdurrazaq, ya buƙaci wata ƙungiyar mazauna unguwar Ɗorayi cikin birnin Kano mai neman hana shi kafa cibiyar shirya finafinai (film house) a unguwar da ta sayi filin nasa ta gina abin da ta ga ya dace.
Furodusan ya bayyana haka ne a saƙon tes da ya turo wa mujallar Fim kan taƙaddamar da ta ɓarke kan niyyar sa ta gina dandalin finafinan.
A kwanan baya ne dai Sultan ya bayyana aniyar sa ta buɗe wani sabon dandalin shirya finafinai mallakin sa a Ɗorayi Ƙarama, Unguwar Bello, Kano.
Sanarwar ta yaɗu sosai a soshiyal midiya, inda aka wallafa hoton wani katafaren gini wanda aka bayyana a matsayin sabon dandalin shirya finafinan.
Sai dai, duk da yaɗuwar sanarwar, Sultan bai bayyana ranar da za a fara aiki ko lokacin buɗe cibiyar ba.
Kwatsam, sai ƙungiyar mazauna unguwar mai suna Ɗorayi Consultative Forum ta bayyana rashin amincewar ta da shirin kafa cibiyar shirya finafinan.
Ƙungiyar ta ce tana nuna damuwa ne kan yiwuwar tasirin da irin wannan aiki zai iya yi ga tarbiyya, tsaro da kuma zamantakewar al’ummar yankin.
Saboda haka ne ta bayyana goyon bayan ta ga ƙorafin da mazauna yankin suka gabatar ga hukumomin da abin ya shafa domin neman dakatar da aikin.
Shugaban ƙungiyar, Abdurrahman Rabi’u, ya ce abin takaici ne yadda wasu ke kallon irin wannan ƙorafi a matsayin hassada, alhali kuwa manufar sa ita ce kare muradun al’umma da makomar su.
Ya ce: “Lokacin da al’umma suka ga wani abu da suke ganin zai iya zama barazana gare su, suna da haƙƙin bayyana damuwar su tare da neman mafita ta hanyar da doka ta tanada. Saboda haka, al’ummar Ɗorayi ba su amince da kafa wannan cibiyar shirya finafinai a yankin ba.”
Ya ƙara da cewa wasu unguwanni da suka fuskanci sauye-sauyen ɗabi’u a baya sun zama darasi ga jama’a, wanda hakan ya sa suke kira da a yi taka-tsantsan kafin amincewa da irin wannan aiki a cikin al’umma.

Bayan samun wannan ƙorafi, wakilin mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Sultan Abdurrazaq kan zargin da mazauna yankin suka yi. Rashin samun sa a waya ya sa wakilin mu ya tura masa da saƙon tes, shi kuma ya aiko da amsa kamar haka: “Rashin sanin mene ne Film House ya sa suke faɗin haka. Ni ba ni da wata matsala da su; idan suna so, su zo su sayi wurin, zan sayar musu, su kuma gina abin da suke so.”
![]()







