ƘUNGIYAR Triple R Kannywood ta kai wa fitaccen jarumin masana’antar finafinan Hausa, Mustapha Musty, tallafin kuɗi naira dubu ɗari biyar (N500,000) sakamakon rashin lafiyar da yake fama da shi na tsawon lokaci.
Tawagar ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin Lawan Ahmad, ta kai ziyarar duba lafiyar jarumin tare da kai masa tallafin a gidan sa da ke cikin birnin Kano a ranar Litinin, 17 ga Agusta, 2026.
A yayin da aka miƙa masa tallafin, sai Musty ya fashe da kuka, inda ya nuna godiya da farin ciki kan wannan karamci da ƙungiyar ta yi masa a lokacin da yake cikin halin rashin lafiya.
Jarumin ya shafe tsawon lokaci yana fama da rashin lafiya, musamman matsalar da ta shafi zuciya, lamarin da ya sa aka kwantar da shi a asibitoci daban-daban domin samun kulawa da magani.
Kungiyar Triple R Kannywood ta bayyana wannan ziyara a matsayin wani mataki na nuna goyon baya da kulawa ga jarumin tare da addu’ar Allah Ya ba shi lafiya, Ya dawo da ƙarfin sa, Ya kuma sauƙaƙa masa halin da yake ciki.
Haka kuma, ana fatan sauran ’yan masana’antar Kannywood da masu hannu da shuni za su yi koyi da wannan mataki wajen tallafa wa abokan aikin su a lokutan ƙalubale.
![]()







