A DAREN yau ne aka yi walimar liyafar cin abinci (wato dina) ra auren fitaccen jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi, da amaryar sa Jamila Abdulnasir wadda ake kira Siyama.
An yi liyafar a Kano kuma ɗimbin ‘yan’uwa da abokan arziki sun halarta.
‘Yan fim sun cika wurin maƙil. Wakilin mujallar Fim ya ga Abdul’aziz Ɗansmall, Nazifi Asnanic, Teema Makamashi, Nasir Naba, Garzali Miko, Naziru M. Ahmad, Sani Musa Danja, Baballe Hayatu, Yusuf Sasen, Abdullahi Amdaz, Isah Adam Feroskhan, Ibrahim Bala, Baba Ari, da sauran su da dama.
Amarya Nuhu da amarya Siyama sun iso zauren bikin

An ci an sha, an yi waƙoƙi da sauran nau’o’i na nishaɗi; kowa ka gani bakin sa kamar gonar auduga.
Ga hotunan amarya da ango nan da wasu mahalarta bikin.






![]()







