• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, August 23, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tallafi: Rarara ya sake raba miliyoyin naira ga ‘yan fim

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
April 30, 2021
in Labarai
0
Tallafi: Rarara ya sake raba miliyoyin naira ga ‘yan fim
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A CI gaba da ya ke yi na taimaka wa abokan sana’ar sa na Kannywood, shahararren mawaƙin siyasa Dauda Adamu Kahutu (Rarara) ya ƙara bada tallafin kuɗi ga wasu matan aure mawaƙa da jaruman Kannywood kimanin su 38.

Wannan shi ne karo na biyu da mawaƙin ya bada tallafin kuɗi ga ‘yan fim; a karo na fim ya raba zunzurutun kuɗi har naira miliyan uku ga jarumai maza da mata su 60 inda ko wannen su ya samu N50,000.

Tallafi na biyu ya sha bamban da na farkon, domin a wannan karon ya kasa tallafin ne zuwa rukuni uku.

Rukunin farko ya ƙunshi maza zalla su 12 waɗanda kowanne zai amfana da N50,000. 

Rukuni na biyu ya haɗa da mata biyu, jaruma da furodusa, inda kowace za ta karɓi N100,000. 

Rukuni na uku ya ƙunshi matan aure mawaƙa kimanin 24 waɗanda kowace za ta karɓi N30,000.

Jimillar su dai za su amfana da naira miliyan ɗaya da rabi.

A jawabin da sakatariyar kamfanin Rarara Multimedia, Rabi’at Sani Umar (Ummin Ibro), ta fitar a Instagram a yau,  ta karanto sunayen waɗanda za su amfana da tallafin tare da bayyana inda kowannen su zai samu kuɗin da aka ba shi.

Ummi ta fara da karanto jerin sunayen maza rukunin farko na tallafin waɗanda su ka haɗa da Baba Hasi, Baba Ƙarami, Idris Shu’aibu Lilisco, Baba Labaran, Baba Ƙarƙuzu, Musa Mohammed Abdullahi, Ɓawo, Malam Dare, Balarabe Jaji, Bankaura, Baba Sogiji da Tijjani Faraga.

Wasu da aka ba tallafin. A sama, hagu zuwa dama: Balarabe Jaji, Shu’aibu Lilisco, Malam Dare. A tsakiya, hagu zuwa dama: Fa’iza Badawa, Ummi Zee-Zee, Murja Baba. A ƙasa, hagu zuwa dama: Naja’atu Ta-Annabi, Balaraba Ramat Yakubu, Tijjani Faraga

Ta ce duk wanda ya ji sunan sa sai ya nemi ita Ummin Ibro domin ya karɓi N50,000.

Rukuni ya ƙunshi sunayen su furodusa Hajiya Balaraba Ramat da jaruma Ummi Zee-Zee, inda su ma aka ce su je wajen Abubakar Bashir Maishadda domin su karɓi N100,000 ko waccen su.

Rukunin ƙarshe mawaƙa ne matan aure, wato Sa’a Sadi, Sa’a Vocal, Zainab Diamond, Naja’atu Ta-Annabi, Murja Baba, Ummi Ahmad Sadi Fari, Luba Jogana, Asiya ‘Yar Sudan, Ummi Fagge, Murjanatu Ambato, A’isha Nagudu, Fati Kawo, Fa’iza Badawa, Maryam Sangandale, Amina Jakara, Sadiya Ali Baba, Fati Solver, Aisha Gwammaja, Safiya Wudil, Husaina Gombe, Fiddausi ‘Yar-Dubai, Zuwaira Isma’il, Suhaima Danko da A’isha Sudan.

An bayyana cewa duk wadda ta ji sunan ta a wannan rukuni ta tuntuɓi Zainab Diamond domin ta karɓi N30,000. 

Idan mai karatu zai iya tunawa, a makwannin baya mujallar Fim ta kawo labarin yadda mawaƙin ya bada  tallafin tsabar kuɗi har miliyan uku ga wasu daga cikin jaruman Kannywood su 60 domin su yi hidimar azumin watan Ramadan. 

Da dama daga cikin jaruman sun yi farin ciki tare da bayyana tallafin a matsayin abu da ya zo a daidai lokacin da su ke cikin buƙatar sa.

Ummin Ibro na karanto sunayen waɗanda Rarara ya ba tallafi

Loading

Tags: Dauda Adamu Kahutu RararaDauda RararaKannywoodRamadan
Previous Post

Cewar Zee-Zee: Maza ku daina da mu na, ina da saurayi na

Next Post

Cewar matan Kannywood: Za mu shirya gagarumar walimar sada zumunci da Sallah

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Cewar matan Kannywood: Za mu shirya gagarumar walimar sada zumunci da Sallah

Cewar matan Kannywood: Za mu shirya gagarumar walimar sada zumunci da Sallah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!