• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Zee-Zee: Maza ku daina da mu na, ina da saurayi na

by DAGA IRO MAMMAN
April 30, 2021
in Labarai
0
Cewar Zee-Zee: Maza ku daina da mu na, ina da saurayi na
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jaruma Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta yi kira ga samari ‘yan bana-bakwai da su daina damun ta da maganar soyayya domin fa ta na da saurayin ta wanda su ke soyayya.

A wani saƙo da ta tura a Instagram, Zee-Zee ta ce wani mutum ya yaɗa labarin ƙarya a soshiyal midiya ya ce wai ta na neman mijin aure.

A cewar ta, hakan ya sa samari ‘yan bana-bakwai, waɗanda ta kira ‘Tom and Jerry’ sun matsa mata da saƙwannin soyayya. Ummi ta ce ita ba masoyi ta ke nema ba domin fa akwai ya ke son ta, ta ke son shi.

Mujallar Fim ta kwafo saƙon da ta tura ɗin, kamar haka:

“Salam to Nigerians. Duk wanda ya rubuta wannan labarin na cewar ina neman mijin aure to ya cuce ni don yanzu ya sa ko wane ‘Tom and Jerry’ sai ya dinga aiko min da hoton sa ta WhatsApp line ɗi na wai zai aure ni, an hana ni sakat; ba hali in hau online na dinga ganin text ‘messages’ masu uban yawa wanda ban isa in iya karanta duka wasiƙun ba da hotunan maza su ma da yawa kala-kala. 

“To dan girman Allah duk wanda ya min wannan tsiyar na cewa ina neman mijin aure ya san kan sa ko ni ban (san) shi ba.

“Saboda haka ka dubi darajan Annabi da Alƙur’ani kada ka sake min ƙarya irin wannan domin maza su na damu na sosai yanzu bayan kuma ina da saurayi na da na ke so shi ma ya ke so na! Haba, mtswwww!”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ba a yau wannan maganar ta fara ba. Kwana huɗu da su ka gabata ne Zee-Zee ta fara maganar cewa an ce wai ta na neman mijin aure.

A wani saƙo da ta wallafa a Instagram, jarumar ta ce: “Ni Ummi Ibrahim Zee-Zee ba ɗan jarida ko wani da ya yi hira da ni na ce masa ina neman mijin aure. Ƙarya ake min domin a ‘followers’ ɗi na daga cikin masu ilimin wanda su ke kula da sa ido a rayuwa ta gaba ɗaya sun san cewar ina da saurayi na da na ke son sa shi ma kuma ya ke so na sosai fiye da kowace mace a duniya bayan mahaifiyar sa, wanda ko gobe na ce ya fito mu yi aure to zai turo iyayen sa gidan mu a mana aure; kawai dai nice ban sa aure a gaba na yanzu ba sai na gama karatu na na digiri domin ni a makaranta diploma kawai na ke da shi.

“Don haka na ji haushi sosai da wannan batun ƙaryar neman mijin  da aka min.

“Kuma abin da ya ban haushi shi ne da aka ce ina neman mijin auren da zai almajira!

“Ni ci da sha tuni na fi ƙarfin su, wasu ma ciyar da su na ke yi. Na gode. A sha ruwa lafiya.”

Kwanan nan ne dai Zee-Zee ta jawo muhawara a soshiyal midiya bayan ta bayyana cewa za ta kashe kan ta saboda wani Inyamiri ya damfare ta zunzurutun kuɗi har naira miliyan 450 a kan wata harkar man fetur da su ka shirya yi.

Mutane da dama sun ƙaryata ta, wasu kuma su ka ce ta faɗi haka ne don ta jawo hankali kawai ganin cewa ba a jin ɗuriyar ta a harkar fim.

Bayan kwana kaɗan kuma aka yi wani rubutu a shafin jarumar na Instagram aka ce wai ta mutu. Bayan kwana biyu kuma sai ga Zee-Zee ɗin ta dawo gida.

Mutane da dama sun ce duk Zee-Zee ce ke shirya wannan abu domin neman suna kawai ko cimma wata manufa.

Kai, wasu ma cewa su ke yi ta zautu, shi ya sa ta ke rubuta irin waɗannan abubuwan “marasa kangado”.

Sanin gaibu sai Allah.

Loading

Tags: KannywoodUmmi Ibrahim Zee-Zee
Previous Post

Buhari ya sake naɗa Adedayo Thomas muƙamin shugaban Hukumar Tace Finafinai

Next Post

Tallafi: Rarara ya sake raba miliyoyin naira ga ‘yan fim

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Tallafi: Rarara ya sake raba miliyoyin naira ga ‘yan fim

Tallafi: Rarara ya sake raba miliyoyin naira ga 'yan fim

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!