• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Babban Hafsan hafsoshi ya ba jarumin dirama Samanja agajin naira miliyan 2

by DAGA IRO MAMMAN
July 5, 2021
in Labarai
1
Babban Hafsan hafsoshi  ya ba jarumin dirama Samanja agajin naira miliyan 2
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BABBAN Hafsan Hafsoshin Sojan Nijeriya (COAS), Manjo-Janar Faruk Yahaya, ya bada agajin kuɗi naira miliyan biyu ga tsohon ɗan wasan kwaikwayo Alhaji Usman Baba Pategi (‘Samanja Mazan Fama), wanda ke fama da rashin lafiya.

Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa an kai wa Samanja tallafin ne a gidan sa da ke Kaduna a yau Litinin.

Rahoton hukumar, wanda mujallar Fim ta fassara, ya bayyana cewa wakilin Babban Hafsan askarawan,  Birgediya-Janar Vitalis Okoro, wato Shugaban Ma’aikatan Kwamanda (GOC) na Runduna ta Ɗaya (1 Division) ta Sojojin Nijeriya da ke Kaduna, shi ne ya kai wa ɗan wasan wannan kuɗi har gida. 

A jawabin da ya aika, Janar Yahaya ya bayyana cewa an sanar da shi halin rashin lafiya da Samanja ya ke ciki, wanda hakan ne ya sa ya ga ya kamata ya taimaka masa.

Ya ce rundunar Sojan Nijeriya na alfahari da kusanta kan ta da fitattun ‘yan ƙasa waɗanda su ka yi kyakkyawan tasiri ga al’umma.

A cewar sa, rundunar Sojan Nijeriya ta ji daɗin yadda Samanja ya riƙa inganta kyakkyawan zato game da rayuwar sojoji ga al’ummar Nijeriya ta hanyar wasan kwaikwayon sa, wanda hakan ya riƙa hasko yadda rayuwa ta ke a cikin barikokin soja. 

Ya ce, “Ta hanyar wannan muhimmiyar rawar da ya taka, ya sama wa kan shi ɗaukaka a fagen harkokin nishaɗantarwa.

Wakilin Babban Hafsan Sojoji, Birgediya-Janar Vitalis Okoro, ya na miƙa kyautar kuɗin ga Alhaji Usman Baba-Pategi (Samanja) a gidan sa a yau Litinin, 5 ga Yuli, 2021.

“Baya ga duk abin da Samanja ya yi na hasko kyakkyawan zato game da sojoji, ya kuma kasance abin so ga rundunar Sojan Nijeriya.”

Cikin farin ciki, Samanja ya maida jawabi inda ya  tuno da aikin soja da ya taɓa yi.

Haka kuma ya ƙara ƙaryata ji-ta-ji-tar da aka yaɗa a kafafen soshiyal midiya a makon jiya cewa wai ya rasu.

Bugu da ƙari, Samanja ya bayyana matuƙar godiyar sa ga Babban Hafsan askarawan saboda wannan kulawa da ya nuna masa.

Daga nan ya yi kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da su zama masu kishin ƙasa kuma su yi addu’ar ci gaba da samun zaman lafiya da juna a ƙasar nan.

Haka kuma ya yi kira ga matasa da a ko yaushe su kasance su na samu abin yi wanda zai amfani rayuwar su. 

Ɗaya daga cikin ‘ya’yan Samanja, Amina Usman, ta bayyana cewa mahaifin ta mutum ne mai kula tare da ƙaunar iyalin sa.

Ita ma ta yi godiya ga rundunar Sojan Nijeriya saboda kulawar da ta yi wa iyalan Samanja.

Idan an tuna dai, a ranar Alhamis ta makon jiya an wayi gari da labarin wai Samanja ya kwanta dama.

Wani tsohon darakta a Hukumar Talbijin ta Ƙasa (NTA) ne ya yi kuskuren rubutawa a shafin sa na Facebook cewa Allah ya yi wa Samanja rasuwa.

Nan da nan labarin ya bazu a soshiyal midiya duk da yakefitaccen ɗan jaridar nan Ibrahim Sheme ya sanar da wanda ya yi rubutun da kuma jama’a cewa Samanja dai na nan da ran shi.

Sheme da ma’aikacin gidan talbijin ɗin nan na KSTV da ke Kaduna, wato Shafi’u Magaji Usman, su na aikin rubuta tarihin rayuwar Samanja, don haka sun san bai mutu ba.

Daga baya dai wanda ya fara bada labarin ya ɗauki gyara, kuma ya goge rubutun nasa tare da bada haƙuri.

Don ƙara dakushe yaɗuwar da labarin ‘rasuwar’ ke yi a soshiyal midiya, Shafi’u ya yi hirar bidiyo da Samanja a gidan sa da ke unguwar Kabala Costain a Kaduna, kuma aka yaɗa bidiyon, wanda hakan ya taimaka wajen daƙili labarin.

A hirar tasu, Alhaji Usman Baba Pategi ya bayyana cewa shi dai ya na nan da ran sa bai mutu ba.

Shi dai Alhaji Pategi, ya fara wasan kwaikwayo tun bayan dawowar sa daga Yaƙin Basasar Nijeriya, inda ya yi aikin soja, kuma ya ci gaba da gudanar da wasan ‘Samanja Mazan Fama’ da na ‘Duniya Budurwar Wawa’ a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna har zuwa lokacin da ya yi ritaya saboda halin manyantaka da kuma rashin isasshiyar lafiya.

Mujallar Fim ta samu labarin yunƙurin da wasu ke yi a yanzu haka domin su yi masa ƙarin agaji saboda halin da ya ke ciki.

Alhaji Usman Baba Pategi a makon jiya
Samanja a lokacin da ya ke cikin ganiyar sa a shirin ‘Samanja Mazan Fama’ na gidan talbijin na NTA

Loading

Tags: Brig.-Gen. Vitalis OkoroChief of Army StaffDuniya Budurwar Wawahausa actorsIbrahim ShemeKannywoodMajor-Gen. Faruk YahayaNigeria ArmySamanjaSamanja Mazan FamaShafi'u Magaji UsmanUsman Baba Pategi
Previous Post

Hotuna: Minista Sadiya a taron shirin ciyar da ‘yan makaranta a Gusau

Next Post

Kannywood: Dalilin yi wa MOPPAN ta Kano kwaskwarima – Jahun

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Kannywood: Dalilin yi wa MOPPAN ta Kano kwaskwarima – Jahun

Kannywood: Dalilin yi wa MOPPAN ta Kano kwaskwarima - Jahun

Comments 1

  1. Jamila Adamu Yaro says:
    5 years ago

    Masha Allah Allah ida nufi. #faroukyahaya #Babapategi #samanjamazanfama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!