JARUMAR Kannywood mai tasowa, Zahra Muhammad (Zahra Diamond), ta yi aure asirce, abin da ya ba mutane da dama mamaki.
Zahra da kan ta ne ta alamta hakan a wani saƙo da ta wallafa a Instagram a ranar Lahadi, 8 ga Agusta, 2021 inda ta ba furodusoshi da daraktoci haƙuri kan rashin ƙarasa masu finafinan su da ba ta yi ba.
Ta ce: “Salam masoya na, ‘producers’ ɗi na, ‘directors’ da abokan aiki na, waɗanda na gama ayyukan su ina musu fatan alkairi, waɗanda kuma ban gama ba ina mai ba su haƙuri, saboda yanayin zaɓin da Allah ke yi wa dukkanin bayin sa, to ya min zaɓi mafi alkairi a gare ni, saboda haka ba ni da baki ko ‘yancin ƙarasa muku ayyukan ku. Fatan za ku fahimce ni? Allah ya ba ku haƙuri ya kuma musanya muku da alkairi.”
Haka kuma ta yi kira ga mamallakan shafukan mabiyan ta da su cire hotunan ta da bidiyoyin ta daga shafukan, domin fa ita ta yi bankwana da harkar fim.

Ta ce, “Don Allah masu ‘fans page’ ɗi na, ku yi haƙuri ku dubi girman Allah ku cire hotuna ɗi na da kuma bidiyo-bidiyo ɗi na, kuma ku canza suna na. Na gode.”
Duk da cewa a wannan saƙon jarumar ba ta ambaci ta yi aure ba, mutane da dama na ganin cewar ta yi aure ne.
Sanarwar ta bai wa jarumai da dama mamaki domin a cewar wasu daga cikin su ko kaɗan ba su kawo wa jarumar aure kusa ba musamman idan aka yi la’akari da yadda a hirar ta da BBC Hausa kwanan nan ta bayyana ƙudirin ta na zama shahararriyar jaruma.
Jarumai da dama sun wallafa hotunan Zahra a shafukan su na soshiyal midiya tare da yi mata fatan alheri.
Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin jarumar kan wannan al’amari, amma haƙar mu ba ta cimma ruwa ba.
Mu na addu’ar Allah ya ba Zahra da sabon mijin ta zaman lafiya da zuriya ɗayyiba.


![]()







