• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Akwai abu uku da ba zan manta ba game da mahaifiya ta, inji Fati S.U.

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 20, 2021
in Labarai
1
Marigayiya Hajiya Hauwa (a hagu) da Fatima S.U. Garba

Marigayiya Hajiya Hauwa (a hagu) da Fatima S.U. Garba

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jarumar Kannywood, Fatima S.U. Garba, ta bayyana cewa akwai wasu abubuwa gudu uku waɗanda ba za ta taɓa mantawa game da mahaifiyar ta ba, wadda Allah ya yi wa rasuwa a shekaranjiya Asabar, 18 ga Satumba, 2021.

Hajiya Hauwa S.U. Garba ta rasu ne da misalin ƙarfe 6:00 na safe a wani asibiti mai suna Adede Specialist Hospital da ke Minna, Jihar Neja, bayan ta yi doguwar jinya.

Ta rasu ta na da shekara 64 a duniya, kuma ta bar ‘ya’ya.

A yayin da ta ke yi wa mujallar Fim ƙarin bayani game da wannan babban rashi na mahaifiyar ta, jarumar wadda aka fi sanu da Fati S.U., ta lissafa manyan abubuwa uku da ba za ta taɓa mantawa da su ba game da Hajiya.

Su ne: kawo ta duniya da ta yi, tarbiyyar da ta yi mata wadda ta sa ta na ɗaya daga cikin jarumai mata masu kamun kai a masana’antar finafinan Hausa, da kuma albarkar da ta sanya wa ‘ya’yan ta a gab da lokacin da za ta rasu.

Jarumar ta ce: “Iyaye su na da muhimmanci a rayuwar ‘ya’yan su gaba ɗaya, amma ba ni da wani a rayuwa ta da ya fi min muhimmaci kamar mahaifiya ta saboda ta zama jigon rayuwa gaba ɗaya.

“Duk da cewa Allah ne ya ke da mutum, amma tarbiyyar da ta yi mani ai ta yi ƙoƙari. A Kannywood ba zan zama ta ɗaya ko ta biyu ba a masu kamun kai, alhamdu lillahi dai. 

“Sannan abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba wanda ta yi min shi ne kawo ni duniya da ta yi; wannan ba zan taɓa mantawa da shi ba. 

“Kuma kafin ta cika sai da ta sa wa duk ‘ya’yan ta albarka, kuma ta ce mana Allah ya sa mu gama da duniya lafiya.”

Ɗimbin ‘yan fim sun taya Fati alhinin wannan rashi da ta yi, kuma sun yi addu’ar Allah ya jiƙan Hajiya.

Fati ta faɗa wa wakilin mu cewa wasu daga cikin ‘yan fim sun je sun yi mata ta’aziyya, amma ba sai ta faɗi sunan su ba, sannan wasu kuma su na kan hanyar zuwa.

To, Allah ya jiƙan Hajiya Hauwa, ya albarkaci abin da ta bari, amin.

Loading

Tags: Fati S.U.Fati S.U. mother's deathFatima S.U. Garbahausa filmsHauwa S.U. GarbaKannywoodMutuwa a Kannywood
Previous Post

Takarar 2023: An maida Ali Nuhu gwamnan Kogi

Next Post

Jarumin Jaruman WAMMA Awards 2021: Gidan Dabino ya sadaukar da nasarar sa ga ma’aikatan ‘Kwana Casa’in’

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Ado Ahmad Gidan Dabino, MON (a hagu) ya na karɓar kambin karramawar sa na Jarumin Jarumai a gasar AMMA Awards ta bana, jiya a Yamai

Jarumin Jaruman WAMMA Awards 2021: Gidan Dabino ya sadaukar da nasarar sa ga ma'aikatan 'Kwana Casa'in'

Comments 1

  1. Shafiu Aliyu says:
    5 years ago

    Allah ya jikanta yayi mata rahama ya gafarta mata

    Allah ya baiwa “Yan uwanta hankurin jure rashinta amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!