SHAHARARREN jarumi Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya sadaukar da nasarar da ya samu ta zama Jarumin Jarumai a gasar mawaƙa da finafinai ta Afrika ta Yamma ga ɗaukacin masu taimakawa wajen tabbatar da shirin nan mai hasko siyasar wannan zamanin, wato ‘Kwana Casa’in’, wanda ake nunawa a tashar talbijin ta Arewa24.
Gasar, wadda a Turance ake kira ‘West African Music and Movie Awards (WAMMA Awards) an gudanar da ita ne a daren jiya a Yamai, babban birnin ƙasar Nijar.

Gidan Dabino ya lashe gasar ne saboda rol ɗin sa na Gwamnan Jihar Alfawa a shirin na ‘Kwana Casa’in’.
Ya samu matsayin ne a ɓangaren Jarumin Jarumai a diramar talbijin mai dogon zango (Best Actor in a TV Series).
An bayyana nasarar tasa ne a gaban ɗimbin mahalarta da ƙarfe 1:00 na dare a babban zauren taro na Palais des congres.

A taƙaitaccen jawabin da ya yi bayan ya karɓi kambin karramawar, Gidan Dabino ya ce ya sadaukar da wannan nasara da ya samu ga ɗaukacin ma’aikatan shirin ‘Kwana Casa’in,’ kama daga kan marubutan labarin har zuwa masu ɗaukar shirin a lokeshin da masu tace shi.
Ya ce, “A madadin dukkanin marubuta fim ɗin ‘Kwana Casa’in’ su tara, da hukumar gidan talbijin ɗin Arewa24 da waɗanda su ke cikin wannan wasa, na sadaukar da wannan kyauta gare su. Ba tawa ba ce ni kaɗai.”

Daga nan sai ya juya ga Jakaden Nijeriya a Nijar wanda ya ke zaune a cikin zauren, ya ce masa, “Mai girma Ambasada, ka dai ga yadda ƙasar mu ta ke ƙoƙari. Mun gode ƙwarai da gaske.”
Masoya da dama sun yi wa jarumin caa, su na taya shi murnar wannan nasara da ya samu.

Ita dai wannan gasa ta WAMMA, ta bana ita ce karo na 7 da aka shirya, kuma majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa mahalarta daga ƙasashe 17 ne su je bikin na bana.
Ban da Gidan Dabino, akwai wasu ‘yan Kannywood ma da su ka lashe gasar a ɓangarori daban-daban.
![]()







