• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, May 5, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Akwai matsala a haramta mana sana’ar fassara finafinan Indiya, inji shugaban masu fassara

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
November 19, 2022
in Labarai
1
Malam Auwal Badi

Malam Auwal Badi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN ƙungiyar masu fassara finafinan Indiya zuwa Hausa na ƙasa, Malam Auwal Badi, ya bayyana cewa dokar nan da Hukumar Tace Finafinai Da Bidiyo ta Ƙasa (NFVCB) ta fitar ta haramcin sana’ar fassararrun finafinan za ta haifar da babbar matsala ga matasa.

Ya ce hakan ya sa tilas masu sana’ar da jami’an hukumar su zauna domin su samo mafita.

Badi ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim a ofishin sa da ke Kasuwar Ƙofar Wambai a Kano.

Ya faɗa mana cewa, “Mun samu wannan umarni kamar yadda Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa ta fitar, amma a yanzu mu na kan zama da su ne, kuma na san za mu cimma matsaya kamar yadda mu ka saba yi a kan duk wasu al’amura idan su ka taso.

“Kuma ka sani, wannan wani abu ne da wasu su ka daɗe su na shirya mana maƙarƙashiya daga cikin mu.”

Shugaban ya ce harkar fassarar finafinan Indiya ba sabuwa ba ce, sun kai kusan shekara goma su na yin ta.

Ya ce masu yi wa harkar zagon ƙasa sun daɗe su na kai ƙarar su don su ga an hana su, amma ba su cimma nasara ba. “Sai kuma a yanzu su ka sake wata hanyar don ganin an hana mu kasuwancin mu,” inji shi.

Badi ya ƙara da cewa: “Ni na san ita hukuma ba za ta yi abin da zai cutar da ‘yan ƙasa ba, saboda haka a matsayin mu na ‘yan ƙasa mu na da damar mu yi kasuwancin mu yadda doka ta tsara.

“Don haka a yanzu ma mu na kan tattaunawa da hukumar tare da lauyoyin mu don ganin an samar da mafita.”

Shugaban ya yi nuni da cewa bai kamata gwamnati ta hana ɗimbin matasa sana’a ba saboda matsalar da hakan zai haifar.

Ya ce: “Babu yadda za a yi a hana sana’ar da mutane sama da dubu ɗari su ke cin abinci a cikin ta.

“Kuma mafi yawan masu wannan sana’ar za ka ga matasa ne, don haka idan har ka hana matasa sama da dubu ɗari sana’a a wannan lokacin, me ka ke ganin zai faru?”

Ya yi kira ga hukumar da ta duba matsalar da matasan za su iya fuskanta da kuma halin da ake ciki a ƙasar nan inda “mutane su na sana’ar ma a yanzu da yaya, ina ga idan aka ce an hana?”

Badi ya ce zama a tattauna a kan matsalar shi ne zai kawo ƙarshen lamarin.

“Domin a yanzu idan hukuma ta hana mu yin fassarar finafinan Indiya da kuma sayar da shi, to su kuma manyan gidajen talbijin da su ke fassarawa su na nunawa fa, su kuma yaya za a yi da su? 

“Don haka ni ina ganin samar da tsari da kuma daidaito a tsakanin mu da Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa shi ne zai kawo mafita, ba hanawar ba.”

Idan an tuna, jami’in hukumar mai kula da shiyyar Arewa-maso-yamma, Alhaji Umar G. Fage, a wata hira da ya yi da mujallar Fim, ya bayyana dalilin hukumar na haramta yaɗa finafinan Indiya da aka fassaro.

A labarin da mu ka buga a ranar 16 ga Nuwamba, 2022, mun ruwaito shi ya na cewa haramcin ba sabo ba ne domin kuwa dokar Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa ta 1993 ta samar da shi.

Alhaji Umar ya ce akwai mutane da ke ƙorafi a kan “yadda wannan fassarar ta ke gurɓata al’adun mu da kuma yaren mu wanda za ka ji ana wasu kalamai na ɓata tarbiyya ko ɓata shi kan sa yaren na Hausa.”

Ya kuma yi nuni da cewa masana’antar Kannywood ta samu koma-baya ta dalilin wannan fassarar da ake yi, har ta kai kasuwancin finafinan Hausa ya durƙushe saboda zuwan fassarar Indiya.

Ya ce tilas ne hukumar sa ta yaƙi wannan fassarar, tunda da man haramtacciya ce, “don su na satar fasahar wasu ne su na sayarwa ba tare da haƙƙin su ba.”

Tuni dai hukumar ta shiga aikin kamen duk wanda ke sana’ar fassarar finafinan na Indiya, inda har ta cafke mutum uku, ta na kuma neman wasu mutum 14, waɗanda da zarar an kama su za a gurfanar da su a gaban kotu domin a yi masu shari’a.

Loading

Tags: auwal badiBollywooddokafassara finafinan indiyaKannywoodkasuwar ƙofar wambailauyoyishari'atace finafinai da bidiyoUmar G. Fage
Previous Post

Kamaye ya yi tir da masu yaɗa ƙarya game da ‘yan Kannywood, ya ce ‘Ina nan ban mutu ba’

Next Post

Abin da ya sa aka gan ni kwance a asibiti – Balarabe Jaji

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Alhaji Balarabe Jaji bayan an masa aiki

Abin da ya sa aka gan ni kwance a asibiti - Balarabe Jaji

Comments 1

  1. Abdullahi GAMAWA says:
    3 years ago

    Gaskiya Bama goyon bayan dakatar da fassara finafinan indiya zuwa Hausa…
    Munfi samun nishaɗi da aka Acikin Wadannan Films, saɓanin na HAUSA..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!