AN bayyana cewa ɗan siyasar nan mai neman zama gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abdulsalam Abdulkareem Zaura (A.A. Zaura), mutum ne mai kyawawan manufofi na yi wa Kannywood garambawul, ta yadda sana’ar shirya fim za ta inganta fiye da yadda ta ke a yanzu.
Babban mai taimaka wa A.A. Zaura a fagen yaɗa labarai, Malam Al-Amin Ciroma, shi ne ya bayyana haka a cikin wata takardar sanarwa ga manema labarai wadda ya fitar a yau game da wasu surutai da su ka ɓullo sakamakon faɗar da ɗan siyasar ya yi ta cewa zai gina katafiyar cibiyar shirya finafinai (film village) a Kano idan an zaɓe shi.
Idan kun tuna, mujallar Fim ce ta wallafa wata hira da ta yi da fitaccen jarumi kuma mawaƙi T.Y. Shaban a madadin A.A. Zaura inda ya ambaci cewa ɗan siyasar ya na da niyyar gina ‘film village’ da nufin haɓaka Kannywood don taimakon matasa su samu aikin yi.
A cewar Ciroma, maganar ta jawo ka-ce-na-ce a wasu shafukan soshiyal midiya tare da “suka ba tare da hujja ba”.
A takardar sanarwar da ya fitar, mai taken “Kyawawan Manufofin A.A. Zaura Dangane Da Masana’antar Fim”, wadda mujallar Fim ta samu kwafen ta, Ciroma ya ce: “Biyo bayan wasu rahotanni da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai da ma zaurukan sada zumunta na zamani cewar mai girma Alhaji Abdulsalam Abdulkareem Zaura (A.A. Zaura), a ta bakin wani fitaccen jarumin Kannywood T.Y. Shaba, cewar ɗan siyasan ya na da niyyar gina katafariyar tsangayar shirin fim na zamani, wato ‘film village’ ne, har ma wasu ke tunanin ana ƙoƙarin kawo matsaloli ne a Jihar Kano, ya sanya mu ka fito da wannan takarda ga manema labarai domin ƙara fahimtar da al’umma yadda lamarin ya ke a bisa ainihin sa, kamar haka:
“1. Mai girma A.A. Zaura ya na da kyawawan manufofi na yi wa masana’antar fim garambawul, ta yadda sana’ar za ta inganta fiye da yadda ta ke a yanzu, saɓanin zancen farko na ginin ‘film village’ da ake suka, ba tare da hujja ba.
“2. Ana kira ga ‘yan adawa masu yaɗa munanan zantuka game da batun ‘film village’ su fahimci cewar Zaura ba shi da niyyar haddasa matsaloli ga al’ummar Jihar Kano, kamar yadda su ke yaɗawa, illa muradin sa na tallafa wa matasa domin kawar da zaman banza, da raɗaɗin talauci da rashin ayyukan yi.
“3. Alhaji Zaura ya yi alƙawari, idan ya cimma burin sa zai tallafa wa masana’antar Kannywood domin inganta sana’ar, ta yadda ‘yan fim za su himmatu ga shirya finafinai nagari, masu wayar da kan al’umma daidai da al’adar Hausawa da kuma uwa-uba gyara tarbiyyar al’umma baki ɗaya.
“4. Ƙofar A.A. Zaura a buɗe ta ke ga masana’antar Kannywood game kowace gudunmawa ta farfaɗo da kyawawan al’adun Malam Bahaushe.

“5. Alhaji Abdulasalam Zaura ya na ƙara kira ga al’umma da su fahimci mahimmancin masana’antar fim da ta waƙa. Ya bayyana cewar ƙasashe da dama, waɗanda su ka ci gaba, su kan yi amfani da masana’antar ƙirƙira wajen samar da ayyukan yi ga matasa, gami da samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnati, tare da biyan haraji.”
Ciroma, wanda fitaccen darakta ne, jarumi kuma ɗan jarida, ya ƙara da cewa, “A bayyane ta ke cewar sana’ar fim da waƙa su na da matuƙar mahimmanci, hatta ga wasu ƙasashen Musulunci. Ana tallafa wa masana’antar ta fuskar wayar da kan al’umma a ɓangarori da dama.
“Saboda mahimmancin su ga al’umar, har kariya ta musamman ake ba su na tsaron lafiyar su.
“Ba wannan kaɗai ba, ko a nan ƙasar, gwamnatoci na sanya ‘yan fim da mawaƙa a fagen wayar da kai saboda mahimmancin su, don haka bai kamata a tashin farko a haddasa matsala ba.
“A ƙarshe, A.A. Zaura na kira ga al’ummar Jihar Kano da su kwantar da hankalin su, su gane cewa ya na da kyawawan manufofi na tallafa wa matasa, da ɗaukacin al’ummar Kano da Arewa baki ɗaya.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa shi dai A.A. Zaura ɗan asalin garin Zaura ne da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano.
Babban ɗan kasuwa ne wanda ke taimakon jama’a, musamman matasa, ta hanyar gidauniyar sa mai suna ‘A.A. Zaura Foundation’.
A.A. Zaura, wanda ɗan shekara 44 ne ya taɓa yin takarar gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar GPN (Green Party of Nigeria), amma a cikin watan Afrilu na bana ya canza sheƙa zuwa jam’iyyar APC bayan wata ganawa da su ka yi da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.