• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ciroma ya yi murabus daga muƙamin ƙungiyar KAFIGAN

by ABBA MUHAMMAD
December 8, 2025
in Labarai
0
Ciroma ya yi murabus daga muƙamin ƙungiyar KAFIGAN

Malam Al-Amin Ciroma

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DARAKTAN yaɗa labarai da harkokin jama’a na sabuwar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya, KAFIGAN, Malam Al-Amin Ciroma, ya aje muƙamin sa.

Al-Amin ya aje muƙamin ne a yammacin jiya Litinin, inda ya aika wa Darakta-Janar ƙungiyar da Ciyaman na Kwamitin Amintattu (BoT) da takardar aje muƙamin nasa.

A cikin takardar, Ciroma ya ce, “Akwai lokuta a rayuwa da zuciya take magana fiye da duk wani muƙami, kuma fiye da tarihin da muka taɓa taimakawa wajen gina shi. Rubuta wannan takarda na daga irin waɗannan lokuta masu nauyi, masu motsa rai, gaskiya, masu ɗan ɗaci kaɗan.”

Ya ci gaba da cewa, “Ina ba da sanarwar aje muƙami na a matsayin memba na Kwamitin Amintattu (BOT) da kuma matsayin Daraktan Yaɗa Labarai da Harkokin Jama’a na KAFIGAN, wanda zai fara aiki nan take.”

Ya ce: “Tun daga kwanakin farko, lokacin da KAFIGAN take a matsayin wani babban buri da aka fara tattaunawa a tsakanin masu hangen nesa, zuwa lokacin da ta zama wata ƙungiya mai ƙarfi wadda ke ɗaukar nauyin masana’antar Kannywood, na tsaya ba kawai a matsayin mai halarta ba, sai dai a matsayin ɗaya daga cikin masu tunani da hannun da suka taimaka wajen gina tushen ta.

“Na zuba lokaci, ƙarfi, soyayya, har ma wani lokaci fiye da abin da kowane matsayi ke buƙata. Na yi hakan cikin farin ciki, domin KAFIGAN ba kawai ƙungiya ba ce; kira ne a zuciya.

“Amma kamar yadda magabata suka ce, ko manyan ginshiƙai ma kan buƙaci hutu. Ayyuka na na ƙashin kai da na ofis sun yi yawa matuƙa, sun kai matakin da suke buƙatar cikakkiyar kulawa na.

“Abin baƙin ciki, waɗannan ayyukan sun hana ni damar ci gaba da ba KAFIGAN kulawar da ta dace da ita da cikakkiyar jajircewa. Zai zama rashin adalci a gare ni da kuma ƙungiyar in ci gaba da riƙe wannan matsayi alhali hannuwa na sun cika da nauyin al’amura masu yawa. Allah Ya ba mu nasara kan lamuran mu, amin.”

Ciroma ya ce, “Kuma a gaskiya, e, akwai motsi da taɓawa a zuciya, wataƙila wannan ma hanya ce ta rayuwa ta na tuna min cewa duk abin da mutum ya bayar, ya kamata ya san lokacin da ya ja da baya, ya huta, ya bar tafiyar ta ci gaba ba tare da shi ba.

“A ƙarshe, babu wata ƙungiya da ya kamata ta dogara sosai ga mutum guda, ko da kuwa shi ne ya taimaka wajen gina rufin da tubalin ta.

“Amma a sani dai, fitar da na yi ba fitar zuciya ba ce. Soyayya ta, girmamawa da fata na alheri ga KAFIGAN suna nan daram. Zan ci gaba da murnar cigaban ta, har daga nesa, amma da irin alfahari na a matsayin wanda ya san abin da aka yi, abin da ya ci, da abin da ya ƙunsa.

“Ina roƙon Allah ya ci gaba da bai wa KAFIGAN cigaba, haɗin kai da hikimar shawo kan ƙalubale. Allah ya ba ta ƙarfi a cikin mutanen ta, natsuwa a cikin shugabancin ta da ɗaukaka a aikin ta. Ina yi maku fatan alheri tare da addu’ar Allah ya ba ku nasara.

“Na gode da damar da ku ka ba ni, zumunci da kyawawan tunani. Ina ja da baya cikin ladabi, godiya da murmushi mai sanyi. Allah bar zumunci.”

Loading

Tags: Al-Amin CiromaKAFIGANmurabus
Previous Post

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

Next Post

Abin da ya sa na buɗe kantin kayayyaki – jarumar Kannywood Fauziyya Maikyau

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Abin da ya sa na buɗe kantin kayayyaki – jarumar Kannywood Fauziyya Maikyau

Abin da ya sa na buɗe kantin kayayyaki - jarumar Kannywood Fauziyya Maikyau

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!