• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tarayya ta umurci sinimu na zamani da su riƙa nuna finafinan Kannywood

* Alkanawy ya lissafa alfanun ga furodusoshi

by ABBA MUHAMMAD
July 12, 2024
in Labarai
0
Gwamnatin Tarayya ta umurci sinimu na zamani da su riƙa nuna finafinan Kannywood

Shugaban NFC, Dakta Ali Nuhu, ya na jawabi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC) ta ƙaddamar da wani gagarumin yunƙuri na ganin ana nuna finafinan Kannywood a gidajen sinima na zamani da ke arewacin ƙasar nan.

Ta yi hakan ne a wani taro da shugaban ta, Dakta Ali Nuhu, ya yi tare da masu ruwa da tsaki a kan harkar sinimu na zamani da daraktoci da furodusoshin Kannywood.

An yi taron a wurin cin abinci na otal ɗin Seelantro da ke Magajin Rumfa, Kano, a ranar Asabar da ta gabata.

Darakta Ahmad S. Alkanawy, wanda ya halarci taron, ya shaida wa mujallar Fim abubuwan da su ka tattauna a wurin taron, ya ce, “Ali Nuhu, a matsayin sa na Shugaban Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya, shi ya shirya taron. Ya kira dukkan masu sinima.

“‘Silverbird’ sun zo tun daga Legas, sun turo wakili, sinimu na zamani, ba irin namu na da ba. Akwai su yanzu da yawa; akwai ɗaya a Katsina, akwai guda biyu a Kaduna, akwai guda uku a Kano, akwai guda biyu a Abuja, akwai guda ɗaya a Adamawa. Amma kuma ba su nuna fim ɗin Hausa Hausa yawanci.

“To shi ne ya ce doka ta ba da damar a nuna finafinan Hausa. Su na fakewa da cewa su na nuna fim ɗin Nollywood.

“Kuma an kafa kwamiti da zai duba ingancin finafinan da kuma me finafinan Hausa su ka rasa wanda ya sa ba a nunawa.

Ali Nuhu (na farko daga dama) tare da mahalartan taron

“A cikin kwamiti ɗin an sa wakilan masu sinima ɗin, wakilin daraktoci, wakilin furodusoshi, wakilin Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, wakilin Hukumar Tace Finafinai ta Jiha da wakili da Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya, aka haɗa kwamitin mutum sha ɗaya, kwamitin har ya yi zama biyu.

“Kuma da ma shi ya kira ni ya na so in shiga ciki. S ƙarshe dai ni ke jagorantar kwamitin.”

Da wakilin mu ya tambaye shi ko wane irin cigaba Kannywood za ta samu daga wannan zama da aka yi, sai Alkanawy ya amsa da cewa, “Zai kawo cigaba da yawa gaskiya, tunda ana maganar a yanzu akwai ‘screen’ za a rinƙa nuna finafinan Hausa, minimum of two weeks.

“Ka ga misali, a ‘screen’ ashirin idan mutum ya yi ƙoƙari ko da dubu ɗari biyar ne sau ashirin, ka ga miliyan goma kenan a sinima. Ana kuma maganar in fim ya karɓu sosai ka na iya neman ‘Amazon’ ko ‘Netflix’ ko kuma wani distribution company. Ya danganta da ƙoƙarin da mutum ya yi don fim ɗin nasa ya yi kyau da kuma kayan aiki na zamani.

“Dole fim ɗin ya zama ya na da abubuwa guda uku: akwai kayan aiki na zamani, sannan a samu labari mai kyau wanda zai ƙayatar, sannan a samu darakta wanda zai yi aiki mai inganci.

“In-sha Allah in waɗannan abubuwa guda uku su ka haɗu, mu na sa ran za a samu cigaban da ake buƙata.”

Malam Ahmad Salihu Alkanawy ya na jawabi
Mahalartan taron

Daga ƙarshe ya ce, “Shawara ga ‘yan’uwa ‘yan Kannywood ita ce, tunda ga abin nan a buɗe, ba wanda za a ce an zaɓi wannan ba a zaɓi wannan ba.

“Abin da mu ke cewa kamar shiga makaranta ce, a ce ga adadin ‘subjects’ da ake so ka ci, ko ka na so ka shiga jami’a ko ka na so ka karanta kaza. Wanda ya ke so ya ci gajiyar wannan abu, to ya inganta aikin sa.

“A wurin mun ba da shawara, wanda ba shi da isasshen jari, su yi haɗin gwiwa, wanda kowa zai mora. Maimakon mutum ya ja tunga ya yi nasa shi kaɗai ba a samu nasarar da ake buƙata ba, gara a haɗa kai kowa ya zo a haɗa ƙarfi da ƙarfe a yi mai kyau guda ɗaya.”

A ɓangaren uban gayyar kuwa, wato Ali Nuhu, da ya yi magana a kan taron a shafukan sa na soshiyal midiya ya ce, “Yin hulɗa da masu ruwa da tsaki na Kannywood, masu baje koli, da hukumomin gudanarwa a yau ƙwarewa ce mai fa’ida da wayewa.

“Mun magance matsalolin da ke fuskantar gidajen sinima a Arewa, inda mu ka binciko hanyoyin shawo kan ƙalubale da share fagen cigaba. Ba a rana ɗaya aka gina birnin Rum ba, amma ƙoƙarin haɗin gwiwar mu ba shakka zai haifar da ingantaccen yanayin finafinai.

Wasu mahalartan taron su na furta albarkacin bakin su

Fitowar sabbin gidajen sinima kamar ‘Silverbird’ da ‘Dex Cinema’ a Kano, Kaduna da Katsina tare da waɗanda ake da su kamar ‘Platinum’ a Kano, ‘Fasnet Cinema’ a Yola da ‘Canal’ a Maraba na nuni da makoma mai albarka.
“Wannan cigaban ya na nuna yiwuwar yankin na zama cibiya mai fa’ida ga masu sha’awar finafinai su na ba da gogewa iri-iri da haɓaka.”

Ali ya ƙara da cewa, “Tattaunawar da mu ka yi ta sake tabbatar da ƙudiri na na tallafawa da kuma ciyar da harkar fim gaba a Arewacin Nijeriya ta hanyar aiki da haɗa hannu da hannu, za mu iya ƙirƙirar yanayi inda ƙirƙira za ta bunƙasa kuma mafarkin sinimu ya tabbata.

“Hanyar da ke gaba ta na da haske, kuma ina jin daɗin ganin tasirin ayyukan mu na gama gari.”

Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa daga cikin cigaban da Ali Nuhu ya kawo bayan naɗa shi wannan muƙamin, ya yi nasarar sake buɗe ofisoshin hukumar da ke Kano da Kaduna, waɗanda sun daɗe a rufe ba su aiki.

Loading

Tags: Ahmad AlkanawyAli Nuhugidajen sinimaHukumar Shirya Finafinai ta NijeriyaKannywoodNFCsinimuTaro
Previous Post

Sadiya Gyale ta tare a ɗakin mijin ta a Kaduna

Next Post

Kwaɓa a ‘Labarina’: Ma’aikatan jinya na so darakta Aminu Saira ya ba su haƙuri

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Kwaɓa a ‘Labarina’: Ma’aikatan jinya na so darakta Aminu Saira ya ba su haƙuri

Kwaɓa a 'Labarina': Ma'aikatan jinya na so darakta Aminu Saira ya ba su haƙuri

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!