Inna lillahi wa inna ilahir raji’un! Babbar ‘yar mawaƙi Ahmad M. Sadiq, wato Habiba, ta rasu.
Ta rasu a ranar Talata da yamma, kuma an yi jana’izar ta washegari a gidan su da ke Medile B, bayan Gidan Kwamishina.
Habiba Sadiq M. Ahmad, wadda ake yi wa laƙabi da Eelham, ta rasu ne tana da shekaru 16 a duniya bayan rashin lafiyar cutar mashaƙo da ta yi fama da ita.
Ahmad dai fitaccen mawaƙi ne da ya yi fice a Kannywood. Shi ne ya yi fitacciyar waƙar nan ta cikin ‘Izzar So’.
Allah ya jiƙan Eelham, ya kyautata makwancin ta.
![]()







