JARUMI Amude Booth, ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayiya Hajiya Zainab Booth, ya ja hankalin dubban mutane da saƙon alhini tare da hoton sa a jikin kabarin mahaifiyar tasa da ya wallafa yau a Instagram.
Fitacciyar jarumar ta rasu ne a ranar 1 ga Yuli, 2021 a asibiti sakamakon rashin lafiya.
Mutuwar ta ta janyo tausayi da addu’o’i daga ɗimbin ‘yan fim da sauran jama’a, musamman saboda kowa ya tabbatar da kyakkyawan halin ta.

Amude, tare da jaruma Maryam Booth, su ne sanannun ‘ya’yan marigayiyar, amma su na da yayye, Shehu da Sadiya.
Amude ya tura saƙon sa ne da Turanci, wanda mujallar Fim ta fassara kamar haka: “Iyaye kan riƙe hannayen ‘ya’yan su na tsawon wani taƙaitaccen lokaci, amma su na riƙe zuciyoyin su har abada. A gaskiya ban gane haƙiƙanin ma’anar kalmomin ‘na yi rashin ki’ ba har sai lokacin da na so in kama hannun mahaifiya ta amma ba ya nan. A rayuwa, mun ƙaunace ki matuƙa, kuma mu na ƙaunar ki har bayan rasuwar ki. Ki na da matsayi a zuciyoyin mu, wanda babu wani wanda zai taɓa cike shi.”
A hoton, an ga Amude a durƙushe a gaban sabon kabarin mahaifiyar, wanda aka kange da ginin bulo.
Ɗimbin mabiyan jarumin a Instagram sun taya shi alhini tare da addu’ar Allah ya jiƙan Hajiya Zainab, wadda ‘yan fim da dama kan kira da sunan Mama Zee.