MATASAN nan da su ka yi takakka da ƙafa daga Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna zuwa Kano domin ganawa da shugaban ƙungiyar 13×13 Movement, fitaccen mawaƙin siyasa Alh. Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), sun samu damar haɗuwa da gwanin nasu.
Mai taimaka wa mawaƙin a ɓangaren soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, ya bayyana cewa matasan, Anas M. Lawan da Mustapha Iliyasu, sun haɗu da Rarara a yau Asabar, 10 ga Satumba, 2022.
Ya ce: “Rarara ya yi masu godiya bisa wannan sadaukarwa da ƙauna da su ka nuna masa.”
Mawaƙin ya yi masu addu’ar Allah ya mayar da su gida lafiya.
Haka su ma sun nuna farin cikin su da burin su ya cika na ganawa da su ka yi gwanin nasu.
Idan kun tuna, Anas da Mustapha ba su samu ganin Rarara a ranar da su ka isa Kano ba saboda ba ya gari, amma sun samu gagarumar tarba daga wakiliyar sa, fitacciyar jaruma A’ishatu Ahmad Idris (Ayshatulhumaira) a madadin sa.
![]()







