• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

MOPPAN za ta agaza wa Rahama A. Ibrahim, sabuwar jaruma da ta musulunta

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
July 30, 2021
in Labarai
0
MOPPAN za ta agaza wa Rahama A. Ibrahim, sabuwar jaruma da ta musulunta
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HAƊAƊƊIYAR ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya (MOPPAN) ta yi alƙawarin samar wa da Rahama A. Ibrahim, wato matashiyar jarumar nan da ta musulunta saboda kallon finafinan Hausa, da kyakkyawan yanayi a Kano, musamman abubuwan more rayuwa.

Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Salisu Muhammad (Officer), shi ne ya bayyana haka a yayin wani zaman musamman da ƙungiyar ta yi da sabuwar jarumar a Kano a yau Juma’a.

Idan masu karatu za su tuna, ɗazu mujallar Fim ta sanar da ku cewa MOPPAN ta ƙudurci gano jarumar don ta karrama ta saboda wannan ƙwazo da ta yi na karɓar Musulunci da kuma bayyana matsayin ta ba tare da wani ɓoye-ɓoye ba.

To, ashe MOPPAN ta naɗa wani kwamiti na mutum biyu domin binciko inda wannan matashiya ta ke tare da tattaunawa da ita kan wasu abubuwa da su ka shafi rayuwar ta da sauran batutuwa muhimmai.

‘Yan kwamitin, Malam Ahmad S. Alkanawy da Salisu Officer, sun kira jarumar sun yi zama da ita inda su ka ji ta bakin ta kan tarihin ta da batun karatun ta, wurin kwanan ta, ƙawayen ta, tarihin rayuwar ta, tushen ta, sauran su. 

Rahama A. Ibrahim a lokacin zaman da ta yi da shugannin MOPPAN ɗazu da yamma

Haka kuma wakilan na MOPPAN sun tattauna da ita dangane da ƙalubalen da ta ke fuskanta tun da ta karɓi Musulunci, da halin da ta ke ciki a yanzu a Kano, da inda ta ke zaune, a hannun wa ta ke, da ma batun ilimin addinin tun bayan karɓar kalmar shahada. 

A wani rahoto da Officer ya kai wa jagororin MOPPAN a guruf ɗin su da ke WhatsApp kan zaman da su ka yi da Rahama, ya sanar da su cewa, “A kuma matsayin mu mun yi ƙoƙarin nusar da ita ‘reality’ na rayuwar Musulunci, mun nusar da ita matsayin ta a yanzu, matsayin wannan masana’anta da mu ‘ya’yan masana’antar a gare ta, sannan mun tabbatar mata da farin cikin kowa a kan wannan yunƙurin ta na neman rabauta. 

“Sannan mun tabbatar mata da cewar za mu kula da lamarin ta domin fatan mu ta zama ‘role model’ a wannan masana’anta, abar kwatance, tare da taimaka mata domin samun rayuwa madaidaiciya.”

Wakilin mujallar Fim, wanda ya halarci zaman, ya ruwaito cewa an shafe kusan awa biyu ana yi wa Rahama tambayoyi, inda a ƙarshe aka tashi da ƙudirin za a faɗi lokacin da za a yi zama na gaba domin ganin an samu damar aiwatar da duk abin da ya kamata.

Mujallar Fim ta fahimci cewa a zama na biyun da za a yi da jarumar, za a gayyato yawancin shugabanni da dattawan Kannywood.

Rahama tare da wakilan MOPPAN, Malam Ahmad S. Alkanawy (a hagu) da Alhaji Salisu Muhammad (Officer) a wurin taron

Loading

Tags: Ahmad S. Alkanawyhausa filmsKannywoodMOPPANRahama A. IbrahimSalisu Muhammad Officer
Previous Post

INEC ta fitar da jadawalin ranakun rajistar masu zaɓe

Next Post

Doka ce ta cire Sunusi Oscar442 daga fim ɗi na ba Afakallah ba – Alhaji Sheshe

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Doka ce ta cire Sunusi Oscar442 daga fim ɗi na ba Afakallah ba – Alhaji Sheshe

Doka ce ta cire Sunusi Oscar442 daga fim ɗi na ba Afakallah ba - Alhaji Sheshe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!