FITACCEN jarumi Mustapha Musty ya bayyana cewa sai da su ka shafe tsawon shekara 13 su na soyayya da Ghadir Mahmud Shareef kafin a ɗaura masu aure a yau.
Musty ya bayyana haka ne a wata tattaunawar musamman da ya yi da mujallar Fim jim kaɗan bayan an ɗaura auren sa da sahibar tasa da ake wa laƙabi da Soha, a yau Lahadi, 29 ga Nuwamba, 2020.

An ɗaura auren da misalin ƙarfe 11:10 na safe a gidan Alhaji Ibrahim D.O. da ke Titin Jakara, kusa da Goron Dutse, cikin birnin Kano, a kan sadaki N50,000.
Taron ɗaurin auren ya samu halartar manyan mutane, ‘yan’uwa da abokan arziki, musamman abokan aikin Musty na harkar fim da su ka haɗa da Misbahu M. Ahmad, Baba Ƙarami, Ado Ahmad Gidan Dabino, Aminu A. Shareef (Momo), Mudassir Haladu (Ɓarkeke), Nasiru B. Muhammad, Nura Mado, Sadiq N. Mafia, da sauran su.
Bayan kammala ɗaurin auren ne mujallar Fim ta tattauna da ango Musty kan wannan aure da ya yi.
Jarumin na Kannywood ya fara ne da bayyana irin farin cikin da ya ke ji game da wannan ranar, inda ya ce: “Gaskiya ina cikin farin ciki saboda wannan rana ce da na daɗe ina jiran ta kusan aƙalla shekaru goma sha uku; sai a wannan rana Allah ya ƙaddara zuwan ta, ka ga ai farin ciki ba zai misaltu ba.
“Kamar yadda ka ga yadda aka halarci taron, gaskiya ba zan iya misalta ma farin cikin da na ke ciki ba gaskiya.”
Musty ya bayyana wa mujallar Fim tarihin haɗuwar sa da Ghadir, ya ce sun haɗu ne ta hanyar wani abokin sa mai suna Aminu Jega.
Ya ce: “Wata rana mu na zaune a Zoo Road, Gidan Ɗan’asabe, sai ya ke gaya min akwai wasu masoya na su na so su zo mu gaisa. Sai na ce masa to ba damuwa, in ya samu lokaci sai ya kawo su.
“Ai kuwa bayan kwana biyu, wajajen ƙarfe 5, wato da yamma, sai ga shi ya kawo su a mota ita da ƙanwar ta.
“Ya kira ni mu ka gaisa a nan shagon Baba Ƙarami, har ta kai dai mun yi musayar lamba da nufin za ta dinga kira na, ni ma haka. Na ce to ba damuwa tunda ita ai masoyiya ta ce, mai son kallon finafinai na.

“Daga nan dai mu ka fara waya. Don daren farko ma da mu ka fara waya da ita ba mu san an kirawo sallar Asuba ba! Kuma lokacin ba wai na irin ‘free call’ ɗin nan ba ne, a’a waya ce ta sa kuɗi ta kira ni da shi, mu ka kai har lokacin kiran sallar Asuba!
“Kuma tun daga wannan lokaci zumunci ya fara ƙulluwa har ta kai ga so ya shiga zuciya ta kuma na furta mata kalmar cewa gaskiya ni ina son ta, kuma soyayyar ta fara ƙulluwa a hankali, ga shi yau har ta ginu kuma mun yi aure.”
Haka kuma Musty ya faɗa wa wakilin mu abin da ya sa bai auri ‘yar fim ba. A cewar sa, “Ba wai ba zan auri ‘yar fim ba ko a ce ‘yan fim ba sa auren ‘yan fim. Shi aure nufin Allah ne kamar yadda aka sani, kuma so idan ya riga ya kama ka na son wani, to har in ka na tare da wanda ka ke son nan da wuya ka samu canji na cewa ga wani ka koma ka na son sa, don haka ba zai yiwu ka na son wannan kuma ka ce ka na son wannan ba, ka ga ka yi yaudara kenan. To wannan shi ne dalilin da ya sa.

“Mun shaƙu da juna da ita, wanda kuma tun da mu ka haɗu da ita ban sa wata mace a cikin zuciya ta ba, wai in ce zan aure ta, in ba ita ba. Amma ba wai babu a cikin ‘yan fim da za ka ce ga wacce ba za ka iya aurar ta ba, za mu iya auren ‘yan fim tunda abokan sana’ar mu ne, mun san juna, sun san mu mun san su.
“To ba wai ba za mu auri ‘yan fim ba ne, kawai Allah ya rubuta wannan ita ce mata ta tunda da ma shi aure da mutuwa tare su ke tafiya, ba wanda kuma ya san lokacin ɗaya daga ciki sai Allah.”
Da yake tsokaci game da halayyar amaryar tasa da irin zaman da za su yi, angon ya shaida wa mujallar Fim cewa wannan abu ne mai sauƙi tunda da ma can sun riga sun san halin juna.
Ya ce: “Tunda ba wai zama ne na irin wata biyu wata uku ba, a’a zama ne na tsawon shekara goma sha uku da ita, ka ga ta san hali na, na san nata; ta san abin da na ke so, na san abin da ta ke so; ta san abin da ba na so, na san abin da ba ta so.
“Wannan abin ina ganin sai mu zauna ni da ita mu rungumi abin da Allah ya hore mana da shi, mu zauna lafiya mu yi ibada, domin shi wannan aure ba abu ne na wasa ba, aure ibada ne za mu yi, mu kuma ƙudiri niyya a zuciyar mu na cewa ibada za mu yi don mu kare mutuncin kan mu da rayuwar mu, kuma mu yi haƙuri da juna da ni da ita.”
A ƙarshe, Mustapha Musty ya nuna farin cikin sa da godiya ga dukkan waɗanda su ka halarci ɗaurin auren nasa waɗanda ya ce ba zai iya kama sunan su ba saboda yawan su.

“Wasu sun zo daga nesa, wasu kusa. Kuma na yi mamakin ganin fuskokin da su ka halarci ɗaurin auren duk da wasu ma ban kai musu kati ba, kawai ji su ka yi a rediyo amma su ka zo. Ina matuƙar godiya ga masoya na. Allah ya bar mu tare.
Na gode.”