RANA ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, a cewar masu iya magana. Kamar yadda mu ka kawo maku hira da mu ka yi da yayan fitacciyar jaruma Rahama Sadau, wato Abba Sadau, game da auren sa, to, Allah ya tabbatar da Zainab Musa Yarima ta zama matar sa.
A ranar Asabar, 30 ga Janairu, 2021 aka ɗaura auren na Abba, wanda cikakken sunan sa Haruna Ibrahim Sadau, da santaleliyar amaryar tasa wadda ake yi wa laƙabi da Zee Yarima.
An ɗaura auren ne a masallacin A’ishatu Ɗan’iyan Misau da ke Titin Shagari, a unguwar Badarawa, Kaduna, a kan sadaki N100,000.
Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Yaseen Auwal, Sanusi Oscar 442, Sani Candy, da Yunusa Mu’azu.
Tun a ranar Alhamis, 28 ga Janairu, aka yi wasan ƙwallon ƙafa a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna, inda aka buga wasa tsakanin ‘yan Kannywood da abokan ango.
Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci wasan ƙwallon sun haɗa da Umar M. Shareef, Sadiq Sani Sadiq, Ubalen Danja, da Tukur Musa (TK). TK shi ne ya ɗauki nauyin shirya wasan ƙwallon, inda abokan ango su ka ci ‘yan Kannywood.


Bayan an ɗaura aure, sai aka ɗunguma zuwa gidan cin abinci ɗin nan na Rahama Sadau mai suna ‘Sadauz Home: da ke Titin Raɓah, aka yi walima.
Haka kuma a daren ranar Asabar ɗin, an shirya gagarumar dina a gidan su Abba da ke Titin Jabi, Unguwar Rimi, wadda an yi ta ne a gida sakamakon dokar rashin bada ɗakunan taro da gwamnati ta saka saboda annobar korona.
An saka lokaci za a fara dinar da misalin ƙarfe 8:00 na dare, amma ba a fara ba sai wajen ƙarfe 10:00 na dare.
‘Yan fim da mawaƙa sun baje kolin su a wurin.
Mawaƙan da su ka nishaɗantar da taron sun haɗa da Umar M. Shareef, Ado Isah Gwanja, da Usman Umar (Sojaboy).
A wurin dinar an ware lokaci da aka ba ango da amarya dama su ka yanka kek, su ka ciyar da junan su.


Bayan yanka kek ɗin, ango ya fara ciyar da amarya, sannan ya ba ƙanwar sa Rahama da ƙawayen ta Fati Washa da Maryam Aliyu (Madam Korede) kek ɗin a baki kamar yadda ya ba amaryar sa.
Iyayen Abba da ƙannen sa su ma ba a bar su a baya ba, domin duk su na wurin dinar, kuma sun yi hotunan nuna ƙauna gwanin ban-sha’awa.
‘Yan fim da su ka halarci dinar sun haɗa da Falalu A. Ɗorayi, Yaseen Auwal, Usman Umar (Sojaboy), Umar M. Shareef, Yusuf Haruna (Baban Chinedu), Mubarak Umar, Sulaiman Sir Zeesu, Jamilu Away Man, Yunusa Mu’azu, Aminu Mirror, Kabiru Zango, Fati Washa, ZPreety, da Maryam Aliyu (Madam Korede).
Bikin ya ƙayatar da ‘yan kallo matuƙa.
Haka aka tashi kowa na yi wa sababbin ma’auratan fatan Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.
A yanzu dai ‘ya’ya mata na gidan Alhaji Ibrahim Sadau waɗanda ake kira ‘Sadau Sisters’ sun tashi daga huɗun da aka sani sun zama biyar, ma’ana Rahama, Zainab, Aisha, Fatima, to kuma da amaryar Abba Sadau, Zainab Musa Yarima Sadau.





