ƘUNGIYAR Ƙungiyoyin Masana’antar Finafinai ta Kannywood a Nijeriya (KAFIGAN) ta ƙaddamar da sababbin shugabannin ta na reshen Jihar Katsina da aka zaɓa, tare da karrama wasu fitattun mutane saboda gagarumar gudunmawar da suka bayar wajen bunƙasa masana’antar.
Hakan ya gudana ne a wani gagarumin biki da aka gudanar a yau Talata a Banquet Hall da ke tsohon Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, a birnin Katsina.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga masana’antar nishaɗi da kuma baƙi daga jihohin Kano, Kaduna da Katsina.
Shugabannin ƙasa na KAFIGAN sun samu wakilci ta hannun Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa, Kwamared Lawal Rabe Lemoo, wanda ya wakilci Shugaban ƙungiyar na Ƙasa, Hon. Adamu Bello Ability, wanda bai samu damar halartar taron ba.
A jawabin sa, Kwamared Lawal ya sake jaddada aniyar ƙungiyar ta ƙarfafa ƙwarewa, haɗin kai da haɗin gwiwa a tsakanin masu sana’ar fim.
Haka kuma ya miƙa kundin tsarin mulkin ƙungiyar da takardar shaidar amincewa ga sabon Kodinetan Jihar Katsina, Aminu Musa Bukar, a matsayin alamar amincewa da reshen jihar a rubuce ƙarƙashin shugabancin ƙasa.
Barista Suleman Abdullahi ne ya jagoranci rantsar da sababbin shugabannin ƙungiyar, waɗanda suka haɗa da Aminu Musa Bukar a matsayin Kodinetan Jiha, Yasir Abubakar a matsayin Sakatare, sai sauran membobin kwamitin gudanarwa da suka haɗa da Hassana Muhammad, Ibrahim Shehu, Auwal Bishir (Malan A), Abdullahi Sani (Dutsin-ma), Ibrahim Suleman Sheme, Yahanasu Ahmad, Kabir Ali, Abdul Musa, Husaina Muhammad, Suleman Isyaku (Rosy), Aisha Lawal (Nayaya), Lawal Sa’idu (Washasha), Ahmadu Sadisu da Shamsu Isa (Dijango).

Har ila yau, an gudanar da bikin karrama wasu fitattun mutane da suka taka muhimmiyar rawa wajen cigaban Kannywood. Daga cikin waɗanda aka karrama akwai tsohon jarumi Aminu Dagash, fitaccen darakta Aminu Mannir, da fitaccen mawaƙi wanda kuma shi ne Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Katsina kan Harkokin Nishaɗi, tare da wasu fitattun mutane da dama.
Baƙi da dama sun gabatar da saƙonnin fatan alheri, ciki har da Kodinetan KAFIGAN na Jihar Kano, Isah A. Isa. Haka kuma, Babban Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Al’adu ta Jihar Katsina, Alhaji Tukur Ɗan’ali, wanda ya wakilci Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, ya yaba wa ƙungiyar bisa ƙoƙarin da take yi wajen bunƙasa fasaha da kare martabar al’adun Arewacin Nijeriya ta hanyar finafinai.
A jawabin sa na karɓar muƙami, sabon Kodinetan Jihar Katsina, Aminu Musa Bukar, ya gode wa shugabancin ƙasa da membobin ƙungiyar bisa amincewar da suka nuna masa da sauran sababbin shugabanni.
Ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru domin inganta ƙwarewa, haɗin kai da walwalar masu sana’ar fim a Katsina, tare da ci gaba da bunƙasa masana’antar Kannywood baki ɗaya.
An kammala taron cikin shagulgula da wasannin nishaɗi da mawaƙa da ‘yan barkwanci suka gabatar, inda membobi da baƙi suka yi murnar fara sabon babi na shugabanci a KAFIGAN reshen Jihar Katsina.
(Mun fassaro daga rahoton Katsina Times)
![]()







