JARUMIN masana’antar Kannywood, Alhaji Rabi’u Rikadawa, ya ba da sanarwar ficewar sa daga ƙungiyar siyasa ta Triple R Kannywood for Renewed Hope, inda ya zama sabon memba da ya bar ƙungiyar cikin ‘yan kwanakin nan.
Rikadawa ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a yau Juma’a, inda ya ce ya fice daga ƙungiyar ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe.
Sai dai jarumin bai bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar barin ƙungiyar ba.
Kafin ficewar tasa, wasu fitattun jaruman da suka haɗa da Mansurah Isah, Ibrahim Birniwa, Abdulkareem Papalaje da Fati K.K. sun riga sun ba da sanarwar ficewar su daga ƙungiyar.
An kafa Triple R Kannywood for Renewed Hope ne domin haɗa jaruman Kannywood da sauran masu nishaɗi masu goyon bayan jam’iyyar APC da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.
Fitaccen mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) shi ne jagoran ƙungiyar. Da yawa sun ce ƙarfin ikon da yake da shi a ƙungiyar ta sa sauran membobin ta sun zama hoto kawai, sai abin da ya ga dama ake ƙullawa.
To amma duk da ficewar tasu daga ƙungiyar, da dama daga cikin waɗanda suka bayyana barin Triple R sun jaddada cewa ba su fice daga APC ba. Sun ce za su ci gaba da mara wa jam’iyyar baya, sai dai ba a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar ba.
![]()







