FITACCEN mawaƙi a Kannywood, Abdulƙadir Tajuddeen, wanda aka fi sani da Abdul D. One, ya bayyana yadda ya fuskanci wata matsala wadda ta kusa yin barazana ga yiwuwar auren sa da yarinyar da zai aura nan da kwanaki biyar masu zuwa.
Za a ɗaura auren Abdul da Ummu-Salma Sulaiman, wadda ake kira ‘Salma Fresh’, da misalin ƙarfe 11 na safe a ranar Lahadi, 12 ga Disamba, 2021 a Kwanar ‘Yan Gana Bus Stop, Layin Transformer, a unguwar Tudun Murtala cikin birnin Kano.
Tun a makon jiya aka fara yaɗa hotunan kafin aure na mawaƙin da sahibar tasa, ana yi masu addu’o’i da fatan alheri.
A yayin da ya ke yi wa mujallar Fim bayani kan yadda ya haɗu da Ummu-Salma, Abdul ya ce, “Mata ta dai ko sahiba kamar yadda ka ambata, amma ni ina ce mata ‘Favourite’, na haɗu da ita a wata unguwa da ake kira Tudun Murtala, sannan kuma ina tare da ita tun shekarar 2019.”
Da yake kusan ko wane neman aure ya kan zo da wata mishkila, wakilin mu ya tambayi angon irin ƙalubalen da shi ya fuskanta wurin neman wannan auren, musamman a matsayin sa na mawaƙi.
Sai ya amsa da cewa, “Na samu ƙalubale sosai, domin tun ranar da mu ka fara haɗuwa da ita, mun samu matsala da yayyen ta. To tun wannan haɗuwar ta farko ba mu ƙara haɗuwa da ita ba, don ba daga haɗuwa ta farko da mutum za ka nuna ka na son shi ba, da sauran su.
“Kuma ko a lokacin da na haɗu da ita da ma ‘fan’ ɗi na ce gaskiya sosai. Don a daidai lokacin mun saki waƙar ‘Kar Ki Manta Da Ni’, to da ma dai ta na bibiyar waƙoƙi na kowane lokaci, sai Allah ya haɗa mu a wurin wani taro.

“Wata rana ba ta da lafiya, ni kuma a daidai lokacin na je Kano, da ma kwana biyu ba na ganin ta ‘online’, sai na ke tambayar ta me ya same ta? Sai ta ce mani ba ta da lafiya ne. Sai na je duba ta.
“A wurin dubiyar da na je, mun samu matsala da yayyen ta maza, shi ma kuma wannan rashin fahimta ne. Amma daga baya da su ka fahimce ni, sai komai ya yi daidai.”
A ƙarshe, mujallar Fim ta tambayi Abdul D. One abin da zai ce game da wannan aure da zai yi, shi kuma ya amsa da cewa, “Alhamdu lillah! Abin da zan ce ina farin ciki sosai, saboda zan auri abin da na ke so ne, kuma ta ke so na.
“Ina farin ciki sosai. Na daɗe ban samu farin ciki irin wannan ba.”
Shi dai Abdul D. One, ɗan asalin garin Dukke ne da ke yankin Ƙaramar Hukumar Funtuwa a Jihar Katsina.
Ya na daga cikin yaran fitaccen mawaƙi kuma jarumi Umar M. Shareef.
Ya samu nasibin waƙa cikin ƙanƙanen lokaci a ‘Shareef Studio’. Yanzu kuma shi ne shugaban ‘AD Music Studio’.
Kamar yadda mu ka taɓa ba ku labari, Abdul, wanda mazaunin Kaduna ne, matashin mawaƙi ne mai farin jini, wanda ya sa ya yi soyayya da ‘yan mata daban-daban.

Soyayyar sa da jarumar Kannywood ɗin nan Sa’adatou Abubakar Marana, ‘yar ƙasar Nijar, ita ta fi jan hankali, amma auren su bai yiwu ba, su ka ƙare da musayar baƙaƙen maganganu saboda kowannen su ya zargi ɗayan da yaudarar ɗayan.
Daf da azumin Ramadan da ya gabata, Sa’adatou, wadda ke zaune a Yamai yanzu, ta bayyana cewa ta yi aure.
Yanzu dai Ummu-Salma ce matar da Allah ya ba Abdul. Da ma Hausawa sun ce matar mutum kabarin sa.


![]()








Comments 1