BAYAN da jarumin barkwanci Ali Artwork ya wallafa hotunan wasu mutane biyu a Instagram da ya ce iyayen Ummi Rahab ne, mujallar Fim ta kira shi domin samun ƙarin bayani, musamman ganin wasu masu karatu na ƙaryata shi tare da yi masa tambayoyi.
Allah cikin ikon sa, sai kuma aka yi sa’a shi Ali Artwork ɗin ya na tare da Yasir M. Ahmad, wato ɗan’uwan Ummi Rahab wanda ke kula da ita a Nijeriya.
Da wakilin mu ya fara tambayar Artwork asalin waɗannan hotunan, sai ya kada baki ya ce, “Ai ga ma ɗan’uwan ta, Yasir, ka yi magana da shi.”
A tsakanin Yasir da Artwork, mujallar Fim ta gano abubuwa da dama waɗanda ba a taɓa jin su ba a da. Misali: sunaye da asalin Ummi Rahab, yadda aka yi yarinyar ta zo Nijeriya, yadda aka yi ta shiga hannun Yasir, dalilin zaman ta ‘yar fim, da asalin sunan ta tunda dai ashe ba ‘Ummi Rahab’ ba ne sunan ta na asali, da batun idan Yasir ya na da aure ko a’a, da halin da ake ciki kan yiwuwar auren ta, da ma sirrin nan na Adam A. Zango da jarumar ta yi barazanar za ta tona idan bai daina shigar mata hanci da ƙudundune ba.
Da farko dai, game da tambayar asalin waɗannan hotuna biyu, kai-tsaye Yasir ya faɗa wa mujallar Fim cewa: “Ai na yi dukkan wani bayani a cikin bidiyon da na yi, ko ba ka fuskanta ba ne? Gaskiya na nuna yadda na ke a wurin ta.”
Daga nan sai Ali Artwork ya karɓi wayar, ya ce, “Ka san shi bai saba irin waɗannan abubuwan ba. Ka san abu aka ce maka na midiya, ba kowa ba ne zai fahimce ka. In ka kula, duk bai san waɗannan abubuwan da kuma yadda ake yin su ba.
“Yasir shi ya kawo ta industiri, domin shi ɗan’uwan babar ta ne. A hannun sa Rahab ta girma, komai da komai ɗawainiyar karatun ta da komai. In ka lura, akwai hoton su tare da kayan makaranta, shi ya ke kai ta makarantar Islamiyya da boko da komai nata.”
Da wakilin Fim ya fara nuna masa cewa akwai masu faɗin mahaifiyar Ummi Rahab ‘yar Nijeriya ce kuma mahaifin ta ne Balarabe, ko kafin wakilin mu ya ƙarasa tambayar sa, sai Yasir ya karɓi wayar ya ce, “Ka na ji ko? Mahaifiyar ta ‘yar Nijeriya ce amma ba ta taɓa zuwa Nijeriya ba. Ni ma a can Saudiyya aka haife ni. Ita Rahab a can aka haife ta. Kashi 80 (cikin ɗari) na ‘family’ ɗin duk su na Makka.

“Wannan da ka gani (a goto) mahaifiyar ta ce, shi kuma mahaifin ta ne. Amma shi ba Balarabe ba ne, ɗan Bangaladash ne; ka san su na shigowa Saudiyya ai, kuma su na aure in sun ga macen da su ke so.
“Saboda haka, wannan mahaifiyar ta ce, shi kuma mahaifin ta ne.”
To shin yanzu ita Ummi za ta ci gaba da fim ne ko kuma saboda wannan matsalar da aka samu za ta dakata da yi tukanna? Sai Yasir ya amsa da cewa, “Gaskiya har yanzu dai mu na nan mu na ta shawara, amma ba mu yanke hukunci ba, saboda ka san mutum da hanyar cin abincin mutum ba za ka hana su ba.
“Amma ni ban taɓa tunanin abin zai zama haka a rayuwar ta ba; da ma ban kai ta ba wallahi. Amma ita ɗaukaka da ma kowacce na zuwa ne da nata ƙalubalen. Ni a matsayin da na kalli abin kenan.
“Kuma in mutane za su yi min adalci, ni ban cika bayyana kai na a matsayin ɗan’uwan Ummi ba. Amma duk duniya ba ta da wanda ya fi ni, saboda tun ta na shekara bakwai mu ke tare da ita.”
Mujallar Fim ta tambayi Yasir batun da ake yi na cewa cewa a yanzu Ummi ta na tare da mawaƙi kuma furodusa Lilin Baba a Kaduna. Menene gaskiyar maganar?
Nan take sai Yasir ya kada baki ya ce, “Inji wa? Gaskiya ba tare ta ke da su ba. A lokacin da ta ke tare da su Adamu (Zango) ta ke aiki me ake cewa? Ta na tare da Adamu ko? In ka ga Ummi tare da su Adamu abu biyu ne: ko ta yi hutun makaranta ta zo hutu saboda wannan yaron nashi Haidar ko kuma ta zo aiki.
“Kuma ka san ya auri wata yarinya Maryam Nas, ita Ummi ɗin ta ɗan je wurin ta sosai in ta yi hutun makaranta. Wannan shi ne.
“Kamar yadda Adamu ya ke a wurin yarinyar nan, haka shi ma Lilin Baba ya ke a wurin ta; aiki ne duka ya haɗa su, matsayin su duk ɗaya ne a wurin ta, babu wanda ya fi wani.
“Ba ta wurin Lili, ba ta wurin Adamu. Duk wanda ya ke neman Ummi, ni zai nema saboda ni kaɗai na san inda Ummi ta ke.
“Saboda na ga abin ya so ya yi yawa, ana so a cuci yarinya, har yanzu Ummi ba ta kai shekara ashirin ba. Ka san kuma mutane ba imani gare su ba. A kan su Adamun nan wani sai ya je ya yi wa yarinya wani abu. Saboda ka ga gani su ke yi kamar ta butulce wa Adamu, gani su ke yi tun fim ɗin ‘Ummi Na’ ta na wurin Adamu ne, amma yanzu ta rabu da shi ta koma wurin Lilin Baba.”
A daidai nan kuma sai Ali Artwork ya sake karɓar wayar daga hannun Yasir ya ce wa wakilin mu, “Akwai ƙarin bayani da na ke da shi, mutane da yawa na ganin kamar mu ke rura wutar rigimar. Gaskiya abin ba haka ba ne.
“Magana ta gaskiya, a kan abin da mutane ba su sani ba, wanda shi Adamu ya ke ɓoye masu, wannan abin ba yanzu ya fara yi ba. Me ya sa duk lokacin da rigima za ta taso da Adamu da mace ne? Ya kamata mutane su bincika. Me ya sa Adamu duk rigingimun da ya ke yi da mace ne?

“To abin da ke faruwa wanda mutane ba su sani ba, mu ka ɓoye, ya so kuma a tona. Kuma abin da ya sa za a tona ɗin gaskiya abin da ya yi wa yarinyar nan yanzu, so ya yi a yi ‘tarnishing image’ ɗin yarinyar nan gaba ɗaya (wato a ɓata mata suna), a yi ‘shutdown’ ɗin ta (wato a kulle ta a daina komai da ita).
“Abin da yayan ta ya faɗa a cikin bidiyon da ya yi shi ne gaskiyar abin da ya faru.
“Amma kuma (Adamu) ya na ‘deceiving’ mutane.
“Ka ga haka ya yi wa Nafisa Abdullahi, haka ya so ya yi wa Rahama Sadau, su Gabon ma duk ya so ya yi masu haka, amma duk su ka kauce. Saboda ta san me ta ke yi. To, duk haka ya ke yi wa ‘yan matan.
“Waɗanda ya yi wa a baya, ba su da bakin da za su iya yi masa wani abu. Da kin taso, su kuma shugabannin masana’antar, masana’antar su ke dubawa, ba wadda aka cuta ba.
“Kuma abin da ba a sani ba, ba Adamu ya cire yarinyar nan a fim ɗin sa ba. Da, wannan yayan nata ya ke kira ya ce masa ya kawo ta, in ba zai samu damar zuwa ba sai ya haɗo ta da wani ta yi aikin ta, su koma gida. Daga baya sai ya koma ya na kira masu yarinya ya ce ta ɗauko hanya ta zo Kaduna. Sai ita ta faɗa wa Yasir, sai shi kuma ya ce mata, ‘A’a, me ya sa Adamu yanzu ba ya kiran mu in zai yi mu’amala da ke?’ Sai ta ce, ‘Aiki ne.’ Sai ya ce, ‘Ba za ki je ba.’ Sai ta ce, ‘Babu matsala, babu inda zan je.’
“Adamu ya kira: ‘Kin taho ne?’ Ta ce masa, ‘Yaya Yasir ya ce ba zan zo ba, sai an kira shi.’
“Adamu ya kira. Sai (Yasir) ya ce wa Adamu sun ga wani canje-canje ne.
“Kuma da ya yi maganar aure, ya ce zai aure ta ne kafin ya ce zai yi fim da ita. To da ma shi Adamu abin da ke faruwa da shi, ya na ‘deceiving’ mutane ne saboda a tausaya masa. Amma kuma shi ba ya tunanin halin da wani zai shiga.
“Yanzu tun da ya je ya yi wannan ‘live video’ ɗin nan, mutum sama da 700,000 su ka yi ‘attacking’ ɗin ta, su na ta zagin ta da ce mata ‘butulu, ‘yar iska, za ki gani, sai mun yi maki kaza!’ Ka ga wannan an jefa yarinyar wani hali, ana yi mata barazana da rayuwar ta.

“Kuma a gaskiyar magana, ya ɓoye wasu abubuwan ne da mutane ba su san da su ba. Kusan abin da ya faru da matar sa kenan ta fim ɗin ‘Nas’. Daga an haɗa su a fim, ya ce ya na so a damƙa masa ita amana. Shekara biyu (da auren su) ya sake ta, yanzu haka ta na nan ba ta da miji. Ka ga ya bar yarinya a gidan su.
“A haka ya na bibiyar ta ya na zuwa gidan su, ya na zuwa inda ta ke. Ka ga wannan ai zalunci ne. To ya daɗe ya na yin abin.”
Shin shi Ali Artwork ko akwai jiƙaƙƙa ne a tsakanin sa da Zango?
Ya ce, “Bari in faɗa maku. Mutane na ganin kamar akwai wata matsala ne tsakani na da Adamu na ke magana a kan shi. Mu ba wani abu mu ke so ba, ya fito ya ƙaryata kan sa a kan wannan magana. Ya fito ya janye kalaman sa a kan yarinyar. In kuma ba janye kalaman sa ya yi ba, har yanzu rayuwar yarinyar na cikin haɗari. In ya janye kalaman sa, sai ya zo mu zauna a yi sulhu.
“Mu na tare da yayan ta ɗin, ya kira shi sau bakwai ko goma ma. Shi (Adamu) so ya ke yi a yi sulhu ta ƙarƙashin ƙasa.”
Shi Adamun ne ya kira Yasir ɗin?
Sai Yasir ya karɓi wayar, ya ce, “Ya kira ni, amma gaskiya ban ɗaga ba, don ba na so ya ja min wani abu wanda ba mu samu mafita ba tsakanin mu.”
Mujallar ta tambayi Yasir ko zai amince idan Zango ya nemi a yi sulhu tsakanin su? Sai ya amsa: “Ai sulhu alkhairi ne. Duk wanda bai rufa wa wani asiri ba, shi ma Allah ba zai rufa masa ba. Yadda ya fito midiya ya yi magana, so na ke ya ƙara fitowa midiya ya yi magana. Wannan shi ne kawai.
“Ni ba so na ke yi a yi ta husumar ba ne, don bai da wani amfani.
A kan masu cewa wai Yasir saurayi mara aure, sai ya ce, “Ina da mata biyu, ‘ya’ya na biyu. Saboda soyayyar da na ke yi wa Ummi, har takwara na yi mata.”
Shin wai ma, ban da Ummi, menene asalin sunan jarumar da ake ta husuma a kan ta?
Yasir ya amsa: “Sunan ta Rahab. Ka san Saudiyya aka haife ta. A nan mu na ce mata Rahama, kuma Rahab ai Rahama ne. Kuma a Saudiyya tunda su na cikin Larabawa su na ce mata Raham. Raham shi ne asalin sunan; wannan ‘Rahab’ ɗin da ake kiran ta da shi yanzu shi Adamun ne ya maida mata shi haka.”
Yasir ya kuma bayyana yadda a cewar sa Zango ya taɓa buɗe wa Rahab shafi a Instagram domin ya riƙa sanya ido a kan harkokin ta na soshiyal midiya, musamman ta hanyar riƙe kalmar sirrin da ake buƙata a shiga shafin har a karanta saƙonnin kai-tsaye (direct messages) da ake aika mata. A cewar sa, wannan ne asalin kunno wutar rigimar ake yi yanzu lokacin da Zango ya karanto abin da ya dame shi a taskar saƙonnin ta na sirri.
Ga yadda Yasir ya ba mu labarin: “(Adamu) ya taɓa buɗe shafin Instagram da sunan ta, ya na saka hotunan ta wanda ya tsinta a gari haka, sannan kuma ba hannun ta ya ke ba, a wannan aikin ne na ‘Farin Wata’, ya dawo mata da shafin a hannun ta, kuma lokacin da ya ba ta shafin bai ba ta ‘password’ da imel ɗin ba, kawai dai ya buɗe mata ta wayar ta, sai ya zamana duk abin da za ta yi ya na gani.
“Kuma a lokacin da ya ba ta shafin, mabiya ba su wuce 14,000 ba, amma sai da su ka kai mabiya sama da 170,000. A lokacin za ka ji an ce an yi ‘hacking’ ɗin shafin, ba ‘hacking’ aka yi ba, ‘disable’ gaba ɗaya aka yi, aka goge shi, saboda ya na ganin duk abin da ta ke yi, hatta ‘dm’ in aka yi mata. Ka ga ko da irin wannan babu yadda za a yi a zauna lafiya.
“Shi ya sa akwai abin da kar ka tsananta bincike a kan shi. Ya ga abin da bai yi masa ba shi ya sa ya goge (shafin). Daga nan ne aka samu sunan ya zama ‘Ummi Rahab’, amma asalin sunan ‘Raham’ ne.”
A kan zurfin ƙaunar da mutane ke yi wa Ummi, Yasir ya ce, “Ummi na da masoya gaskiya, don tun kafin ta fara fim mutane ke son ta. In zan faɗa maka ka yarda, tun kafin fim ɗin ‘Ummi Na’, duk inda Ummi ta shiga za ka ji mutane na cewa su na son ta.”
Bugu da ƙari, Yasir ya bayyana yadda aka yi har Ummi ta shiga harkar fim, ya ce, “Dalilin da ya sa Ummi ta fara fim, tun lokacin da Ali Nuhu ya yi fim mai suna ‘Rai Da Buri’, ta ga Amira ‘yar gida Ali Nuhu (a fim ɗin), fim ɗin ya ba ta sha’awa. Ta ga yarinya ƙarama ta yi fim, kuma ka ga a lokacin ni ma ƙarami ne, don yanzu haka ban wuce shekara 32 ba a duniya. A lokacin ta ke ce min ita fim ta ke so, da sauran su. Ni a lokacin ban san wani ɗan fim ba, ban san kowa ba.
“A haka na rinƙa kutsawa, ina fita ina shiga har na samu ta yi wannan fim ɗin na ‘Ummi Na’.
“Kuma wannan fim ɗin tunda ba aiki na ba ne, ban san Adamu ne zai yi ko Jamila ce za ta yi ko wanene zai yi, ni ban sani ba. A wannan lokacin na ɗauka idan an yi fim ɗin ni ne zan biya. Saboda na sha wahala kafin in samu haka ɗin, kuma wannan lokacin N20,000 aka ba ni.
“In ka dubi labarin, a kan ta ya ke. Idan ka lura, a wancan lokacin ta na amfani da sunan ta ne a matsayin Rahama Yasir. Ko yanzu idan ka duba irin su ‘Ummi Na’, ‘Labiba’, su ‘Sadaka Yalla’ da sauran su, za ka ga duk Rahama Yasir ne, ba wai Ummi Rahab ba ne.”
Shin wai ma, sunan iyayen nata? Da Fim ta yi masa wannan tambayar, sai Yasir ya ce, “Sunan mahaifiyar ta Sarah, ka ga a nan Hausawa na cewa Saratu. Shi kuma mahaifin ta sunan shi Saleh Ahmad. Wannan shi ne taƙaitaccen abin da zan faɗa maka na gaskiya. Duk wani wanda zai faɗi wani abu, bayan wannan ne.”
A kan ji-ta-ji-tar da wasu ke yaɗawa wai iyayen Ummi Rahab sun rasu, Yasir ya ce, “Haka na ga wani Datti Assalafy ya yi rubutu wai babar ta ta rasu, waye-waye. Na kalla na yi dariya na ce, ‘Mutane na kai kan su wuta ba su sani ba!'”
Haka kuma da wasu ke cewa wai Ummi ‘yar zina ce, Yasir ya ce, “Ko da wasu ke cewa an haife ta ne ba tare da aure ba, ƙaddara da gaske ne. Laifin ta ne? Mutane su na faɗin abin da ba su sani ba, kuma wannan kawai sai ya kai mutum wuta. Kuma Allah ba ya yafe laifin wani a kan wani.
“Kuma wallahi yarinyar nan tun da aka haife ta ‘yar gata ce. Don da wani mugun riƙo aka yi mata, da ba a haka za a gan ta ba. Saboda haka, magana ta gaskiya iyayen ta aure su ka yi.”
Amma ko su Yasir su na da tunanin yi mata aure nan kusa? Sai ya amsa da cewa, “Ummi wai? Wallahi Allah ne bai yi ba, da yanzu ta yi aure. Tunda ni da kai na har aboki na na kawo mata, tun kafin ta dawo industiri ta yi wannan fim ɗin ‘Farin Wata’ na kawo mata aboki na, amma aka samu saɓani. Ka san shi aure fa kamar ajali ne.

“Ni yanzu mata na biyu kamar yadda na faɗa maka. Kuma wallahi ban taɓa tsammanin zan same su a lokaci ɗaya ba, domin tsakanin ta farkon da ta biyun wata uku ne kawai.
“Da na haifi ‘ya’ya na, ɗaya sunan ta Ummi, ɗaya kuma sunan mahaifiya ta.”
Yasir ya kuma faɗi yadda aka yi aka ga Ummi a Nijrriya a yayin da iyayen ta su na Saudiyya. Ya ce: Dalilin zuwan Ummi Nijeriya, wallahi ba don komai ba ne illa karatu. Ka san Saudiyya da Nijeriya ba ɗaya ba ne. Yaran Saudiyya da na Nijeriya ma tarbiyyar su ba ɗaya ba ne. Ka san Larabawa, sai ka ga ɗa ya kai uba kotu. Su ba su iya soyayya kamar mu ba. Kuma ka san kowa da irin nashi al’adar. Mu kuma da yake mu na da alaƙa da Nijeriya, kuma ana jin irin tarbiyyar da ake samu a Nijeriya, shi ya sa aka turo ta nan ta zo ta yi karatu, in ta samu miji ma a nan ta yi aure.
“Ai akwai wasu ‘yan’uwan ita Ummi ɗin waɗanda su ke tare a can da yawa an dawo da su nan, wasu ma sun yi aure.
“Ni ma ina da shekara tara aka kawo ni Nijeriya. Ita kuma lokacin da aka kawo ta, ta na da shekara bakwai, don tun da aka haife ta a can Saudiyya ni ba ta taɓa gani na ba, sai dai a nuna mata hoto a ce mata, ‘Ga ɗan’uwan ki.’
“Shekarar ta bakwai a can. Wannan shi ne dai a taƙaice.”
Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Adam A. Zango kan zargin da Artwork da Yasir su ka yi masa amma hakan ba ta samu ba. Mun dinga jin wayar sa a kashe, kuma bai amsa saƙon tes da mu ka tura masa ba har zuwa lokacin wallafa wannan labari.
www.fimmagazine.com
Copyright © All rights reserved
Hm! To Allah shi kyauta
Amma na so da Kun tambayi Yasir dinnan, ko Ina ‘yan uwan uban ita Raham,kuma me yasa shi uban ta bai zabi ya Kai ta wajen nashi ‘yan uwan ba? Tunda a Islam dai ‘yan uwan uba suke da alhakin ‘ya ko Dan Dan uwan su, kafin ayi maganar ‘yan uwan uwa sai in an rasa na Uba, ku tambaya mana.
Allah yasa mudace
Hmm allah yakeuta amma da aurar da wannan yar karamar yarinya raham dinan kukayi dasai yafiyemata mutunci dawannan surutan banzan dakukasayayi
Comment: Allah ya azamu bisa hanya mafi kyau
Gaskiyar amayar da ummi gurin mahaifinta zata fi daraja aduk hannun Wanda ta sauka da aure
Comment: Zakaran fa da Allah ya nufeshi da cara, ko ana ga mazuru ga shaho sai fa ya yi ta. Adamu gurgun doki ne fa, mai hawansa sai ya shirya! Hasken daukakar Adam Zango, ya fi gaban hassadar ‘yantsaki kamarku ya disashe shi. Ku canza wata karyar wannan kam mun ki karba.
Andai yi an gama ummi kuma tayi aurenta saidai kuma abi wani sarkin