• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Adam Zango da Safiyya Chalawa sun samu ƙaruwar ‘ya mace, Furaira Dianah

by DAGA IRO MAMMAN
November 6, 2021
in Ranar Murna
0
Princess Diyanah tare da iyayen ta, Adamu da Safiyya

Princess Diyanah tare da iyayen ta, Adamu da Safiyya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN jarumi kuma mawaƙi Adam A. Zango a yau ya samu ƙaruwa da haihuwar ‘ya mace.

Matar sa, Safiyya Umar Chalawa (Suffy), ta haifi samɓaleliyar yarinyar lafiya ƙalau a asibiti a garin Kaduna.

Zango ya raɗa wa ‘yar tasu suna Furaira, wato sunan mahaifiyar sa, to amma saboda alkunya, an bai wa yarinyar laƙabin Diyanah.

Mujallar Fim ba ta gano asalin wannan laƙabi ba, amma wata majiya ta ce sunan marigayiya Princess Diana ta ƙasar Ingila ne aka sanya mata, musamman ganin cewa ita ma ya yi mata inkiya da ‘Princess’.

Safiyya da Diyanah su na barci jim kaɗan bayan isowar jaririyar duniya

Jarumin ya bayyana labarin wannan sabuwar haihuwar da aka yi masa a soshiyal midiya a yau lokacin da ya wallafa hotuna biyar da bidiyo ɗaya na jaririyar a Instagram.

A sanarwar, ya ce: “Godiya ta tabbata ga Allah s.w.t. Allah ya raya mana ita bisa turbar addinin Musulunci. Allah ya shirye ta, ya sa Annabi Muhammad s.a w. ya yi alfahari da ita ranar lahira.”

Ya ci gaba da cewa, “Sunan ta Furaira Adam. Sunan mahaifiya ta ne! Sunan kunya Princess Diyanah!”

Ɗimbin masoya sun taya Adamu da Safiyya murna tare da addu’ar Allah ya raya Diyanah, kuma ya albarkaci rayuwar ta.

A lissafin da mujallar Fim ta yi, ta fahimci cewa Diyanah dai ita ce ta bakwai a jerin ‘ya’yan Adam A. Zango. A cikin su akwai maza huɗu da mata uku.

Da haihuwar Princess Diyanah har an buɗe mata shafi a Instagram inda za a riƙa wallafa hotunan ta har zuwa nan gaba kamar yadda wasu ‘yan fim ɗin ke yi.

Furaira Adam A. Zango (Princess Diyanah)

An ɗaura Zango da Safiyya ne a Gwandu, Jihar Kebbi, a ranar 26 ga Afrilu, 2019. Ita ce mace ta shida da ya aura, amma ya rabu da sauran biyar ɗin ɗaya bayan ɗaya.

Diyanah ce ‘yar Safiyya ta fari.

Allah ya raya Diyanah, ya albarkaci rayuwar ta, amin.

Loading

Tags: Adam A. ZangoAdam Zango familyFuraira Adam Zangohaihuwahausa filmsKannywoodPrincess Diyanah Adam ZangoSafiyya Umar Chalawa
Previous Post

An zaɓi jagororin Kannywood, Ahmed Sarari da Sani Mu’azu, a matsayin ‘yan kwamitin gudanarwa na ƙungiyar kare haƙƙin manishaɗanta ta Nijeriya

Next Post

Gwamnati ta haramta nuna wani fim kan ‘yan luwaɗi a sinimun Nijeriya

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Next Post
Fostar fim ɗin 'Eternals'

Gwamnati ta haramta nuna wani fim kan 'yan luwaɗi a sinimun Nijeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!